Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da wasu mutane biyu da Hukumar EFCC ta gurfanar a gaban kotu a yau Laraba sun musanta zarge-zargen rashawa na Naira biliyan 80 da ake yi musu.

Yahaya Bello, wanda shi ne na farko a cikin mutanen da ake tuhuma tare da sauran mutanen biyu Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu, sun musanta duka tuhuma 16 da aka fara karanto musu a gaban mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun ta Abuja.

Yahaya Bello da jami'an EFCC

Joseph Daudu, (SAN – babban lauya) shi ne jagoran lauyoyin da ke kare toshon gwamnan da sauran waɗanda ake tuhuma, yayin da Kemi Pinhero (shi ma babban lauya – SAN), ke jagorantar masu gabatar da ƙara.

Bayan musanta aikata laifukan, lauyan waɗanda ake tuhumar ya nemi a bayar da belin Bello amma lauyan EFCC ya nemi kada a bayar da cewa wa’adi ya wuce tun watan Oktoba.

To amma bayan sauraron ɓangarorin biyu kotun ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar belin.

Yahaya Bello

EFCC ta yi nasarar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar ta Kogi a gaban kotun ta tarayya da ke Abuja a yau Laraba bayan wata da watanni na gaza hakan, kasancewar ya ƙi amsa gayyatar hukumar kuma duk yunƙurinta na kama shi ya ci tura.

A jiya Talata ne aka ce tsohon gwamnan ya kai kanshi hukumar ta EFCC da rakiyar lauyoyinsa – amma daga baya hukumar ta ce tana tsare da shi.

By Ibrahim