Mahawarar da masana ilimin dokoki da lauyoyi da ‘yan fafutukar kare hakin dan Adam suka nazarta na nuna wannan tsari ba abu ne da za a zura ido gwamnati na yin yadda ta ga dama ba, abin da yasa a karon farko suka fito suna wannan zama.
Tun a watan Agustan wannan shekarar aka kafa dokar da ke raba mutanen da aka samu da ta’addanci ko manyan laifukan cin amanar kasa da takardun kasa.
Me muhawarar ke cewa?
Masanan da ke wannan muhawarar irinsu Diori Ibrahim, wanda masanin harkokin shari’a ne ya ce sun yi kokarin fahimtar tasirin wannan doka, wanda suka ga kwata-kwata bai dace ba.
Ya ce kowane ɗan ƙasa na da zuri’a don haka akwai rashin dacewa a tsallake hukunce-hukuncen da dama akwai tanadinsu a kore mutum ko rabashi da takardun ‘yan kasa.
“To wani amfani ake son samu daga wannan doka, tunda akwai wasu hukunce-hukunce har na kisa da ake iya yiwa mutum”.
Rabi’u Umaru shi ma wani masani doka kuma lauya da ya gabatar da kasida a lokacin muhawarar da aka gudanar a birnin Yamai, ya ce dukka ‘yan Nijar ba sa na’am da wannan tsari saboda kowa na iya aikata laifi, kuma dokokin ƙasar sun tanadi hukunce-hukunce dai-dai da laifukan da mutum ya aikata.
Don haka wannan ba hanya ce ta bullewa ba, ko samar da zaman lafiya a cikin ƙasar.
“Akwai bukatar a kiyayye wannan doka a cigaba da bin tsarin da suke da shi a baya, saboda wannan doka tayi tsauri da yawa”.
“A matsayina na ɗan ƙasa da na jima ina gwagwarmaya bai kamata a bijiro da wannan doka ba”.
Sai dai mai gabatar da karar na gwamnati, Usaman Baito da ya halarci wannan muhawarar ya ce Nijar ta shiga yanayin da ba ta saba ganin irinsa ba, shiyasa aka kirkiri wannan doka.
Ya ce babu wani abun laifi a wannan doka, saboda bai dace a ce an samu mutum da aikata laifukan cin amana ko kashe mutum ko hada-kai da ƙasashen ketare a zura masa ido ba tare da irin wannan hukuncin ba.
Ya ce duk wanda aka samu da irin waɗannan dabi’u to tamkar ya raba kansa ne da ƙasar ko ya kore kansa da kansa don haka bai ga wani abun cece-kuce a kai ba.
Shi kumwa Dr Hassan Bubakar, tsohon ministan shari’a na cewa dokar gaskiya ta saɓawa tsarin ƙasar, kuma ana yin dokoki ne saboda mutane, ba wai mutane saboda dokoki ba.
Tsohon ministan dai ya ce akwai bukatar a sake zama domin laluben wasu hanyoyi na janye wannan tsari da yake cewa ya yi tsauri da yawa.
Mutanen da dokar ta shafa
A watan Agusta ne Janar Tchiani ya sanya wa dokar korar duk wani ɗan Nijar da aka samu da hannu wajen cin amanar ƙasar rigar kasancewarsa ɗan jamhuriyar wadda ta janyo ka-ce-na-ce ciki da wajen ƙasar.
Tun daga lokacin da aka bijiro da wannan doka zuwa yanzu mutum 19 aka raba da takardunsu na ‘yan kasa a Nijar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta ce dokar wani salo ne na tauye haƙƙin ƴan ƙasar.
Hakan na nufin yanzu dai mutanen da aka kora din ba su da wata ƙasa da za bayyana a matsayin ƙasarsu.
Babu cikakken bayani dai na halin da mutanen da aka korar suke ciki.