Asalin hoton, Abdirahman Aleeli/AP

Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya a yankin Somaliland da ya ayyana cin gashin-kansa daga Somalia, Abdirahman Mohamed Abdillahi (Irro) ya kayar da shugaban ƙasar mai-ci, Muse Bihi Abdi, a zaɓen da aka yi, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar a yau Talata.

Jagoran jam’iyyar hamayya, Waddani – Abdirahman, ya samu kashi 63.92 cikin ɗari yayin da Shugaba Bihi ya ci kashi 34.81 cikin ɗari, na ƙuri’u kamar yadda hukumar zaɓen ta sanar.

An haifi Abdirahman Irro a Hargaisa, babban birnin ƙasar ta Somaliland, ranar 29, ga watan Afirilun 1955, inda ya yi makarantar elimantare a Somalia, kuma daga nan ya je kwaleji a Amurka, har ya yi digiri na biyu a fannin kula da harkokin kasuwanci.

Irro ya yi aikin diflomasiyya a ofishin jakadancin Somalia a Moscow, inda ya fara aikin diflomasiyya a ma’aikatar harkokin wajen Somalia a 1981.

A lokacin yaƙin basasa a 1991 na Somalia ya kasance muƙaddashin jakadan Somalia a tsohuwar Tarayyar Sobiyet.

Daga baya ya tafi Finlad inda ya je ya zauna da iyalinsa a can har ya samu takardar zama ɗan ƙasar.

Irro ya fara shiga siyasar Somaliland a 2002, a jam’iyyar UCID.

Ya kasance shugaban majalisar dokokin Somaliland tsawon shekara 12 daga 2005.

Irro ya kafa jam’iyyar Waddani a 2012, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2017, amma ya sha kaye a hannun Muse Bihi Abdi.

A wannan shekarar kuma ya sake yin takarar inda ya yi nasarar kayar da shugaban mai-ci.

Somaliland ta kasance ƙarƙashin mulkin kanta da ta ayyana tun bayan da ta sanar da yankewa daga Somalia a 1991.

Sai dai har yanzu ba ƙasar da a duniya ta amince da ita a matsayin ƙasa nai cin gashin-kanta, wanda hakan ya taƙaita mata samun kuɗaɗe daga waje da kuma ƙalubale ga al’ummarta miliyan shida wajen tafiye-tafiye.

By Ibrahim