Asalin hoton, Reuters

Sir Keir Starmer ya gana da shugaba Xi Jinping a taron kasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziki na G20, inda ya jaddada muhimmancin “dangantakar Birtaniya da China” ga kasashen biyu.

Ganawar ita ta farko da wani firaministan Birtaniya ya yi da shugaban na China tun shekarar 2018, bayan da dangantaka ta yi tsami a baya-bayan nan.

Sir Keir ya taɓo batun ɗan rajin kare dimokradiyya a Hong Kong, Jimmy Lai da ake tsare da shi, yana mai cewa ya damu da rahotannin “tabarbarewar” lafiyarsa.

Har ila yau, firaministan ya nuna sha’awar samun babban haɗin gwiwar kasuwanci, musamman kan “bangarorin da za su inganta kasashen biyu” kamar zaman lafiyar ƙasa da ƙasa, da sauyin yanayi da ci gaban tattalin arziki.

Sir Keir ya gana da shugaba Xi a gefen taron G20 a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, kuma yayin da yake magana a farkon taron, ya ce: “Muna son dangantakarmu ta kasance mai ɗorewa kuma amintaciya, kamar yadda muka amince, da kaucewa duk abubuwan da za su iya sanyawa mu shammaci juna, idan har za mu iya.”

Yayin da batun goyon bayan da China ke bai wa Rasha a yaƙinta da Ukraine ya haifar da suka daga Birtaniya da sauran ƙasashen yammacin duniya, Firaministan ya kuma ce yana son a tattauna cikin aminci a kan ɓangarorin da ƙasashen biyu ba su sami jituwa a kai ba, da suka hada da batun Hong Kong, da hakkin ɗan’Adam da yaƙin Rasha da Ukraine. .

By Ibrahim