'Yansandan Najeriya

Asalin hoton, Reuters

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Ogun ta tabbatar da kama mutum 21 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri, ciki har da sojojin ƙasar biyu yayin wani samame kan wani otel a birnin Abeokuta.

Kakakin rundunar a Ogun, Omolola Odutola, ya bayyana cewa an kai samamen ne ranar Juma’a bayan samun bayanan sirri game da taron mambobin ƙungiyar Aiye.

Daga cikin abubuwan da suka karɓe daga hannun mutanen akwai bindiga ƙirar gida, da gatari, da shuɗayen huluna masu yawa, da sauran kayayyakin da masu asiri ke amfani da su.

“Tuni aka miƙa mutanen ga sashen binciken laifuka da ayyukan asiri domin ci gaba da bincike,” in ji kakakin.

By Ibrahim