Asalin hoton, AFP
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, musamman a arewa ta tsakiyar ƙasar.
NiMet ta sanar da hakan a cikin hasashen yanayi na watan Yuni na shekarar 2025, wanda ya fara aiki a ranar Lahadi da ta gabata.
Wannan rahoton na zuwa ne yayin da ƙasar ke fuskantar mummunar ambaliya da ta faru a jihar Neja wadda ta jawo asarar rayuka sama da 500.
NiMet ta ce duk da yanzu ne damina ke kankama a yankin arewa, ana hasashen ruwan sama a cikin ƙanƙanin lokaci a wasu jihohin kamar Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da kuma yankin Babban birnin tarayya (Abuja).
“Wannan na iya haifar da ambaliyar ruwa a wuraren da ke cikin haɗari,” in ji rahoton na NiMet.
Rahoton ya shawarci mutane su kasance cikin shiri da kuma lura da bayanan da hukumar ke fitarwa akai akai.
Hakanan niMet ta buƙaci hukumomin kula da madatsun ruwa su sanya ido sosai tare da kula da cikowar ruwa a madatsun.
An nuna cewa jihohin kudancin ƙasar da na arewa ta tsakiyar ƙasar za su fuskanci ruwan sama mai ƙarfi da iska a kai a kai.
Duk da haka, NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Niger, Nasarawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Edo, Delta da Abuja ba za su sami ruwan sama mai yawa kamar yadda suka saba ba.
Wannan ya sa hukumar ta shawarci manoma su yi amfani da ilimi da ƙwarewa wajen harkokin noma.