Atiku Abubakar/X

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa a cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a Najeriya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa, Atiku ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ba za ta yi shiru ba yayin da halin rayuwa ke ƙara tsananta ga ‘yan kasa tare da yawaitar almubazzaranci daga bangaren gwamnati.

Ya ce babu wata gwamnati da ta taɓa jefa al’umma cikin irin wannan ƙunci ba tare da la’akari da gaskiya da rikon amana ba.

“Wannan gwamnati ta Tinubu ba wai kawai ta ƙara talauci a fadin ƙasar ba ne, har ma ta kafa sabbin tarihi wajen almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.”

Atiku ya ƙara da cewa a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, jami’an gwamnati suna rayuwa cikin walwala, suna amfana daga kasafin kuɗi da ke amfana kawai ga attajirai yayin da talakawa ke ci gaba da shan wahala.

“Abin taƙaici ne yadda Najeriya ba wai kawai ta kasance ƙasa mai fama da matsanancin talauci ba, yanzu haka ta zama ƙasar da ke da yawan yara masu fama da rashin abinci fiye da kowacce ƙasa a Afirka.” in ji Atiku.

Ya ce bisa rahoton Global Hunger Index na 2024, Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa da rashin abinci, inda take matsayi na 18 a duniya.

Atiku ya ce duk wani tsarin gwamnati da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan mulki ya fi cutar da talakawa fiye da komai, yayin da masu kuɗi ke ci gaba da morewa.

Duk wani abin da ya fi tayar da hankali shi ne yawan bashin da gwamnati ke ci gaba da karɓa.

“A lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, jimillar bashin ƙasar ya tsaya kan naira tiriliyan 49. Amma cikin shekaru biyu kacal da fara mulki, ya karu zuwa tiriliyan 144.”

Atiku ya ce su a matsayin jam’iyyar adawa, ba za su zuba ido ba su kalli abubuwan da ke faruwa ba su ci gaba.

By Ibrahim