Asalin hoton,
Getty Images
Wata babbar kotu a Legas ta yanke hukuncin kisa ga direban motar bas, Andrew Ominikoron, kan kisan wata budurwa mai shekara 22, Bamise Ayanwola.
A zaman kotun na fiye da awa biyu da rabi, mai shari’a Serifat Sonaike ta ce kotun ta tabbatar da cewa mutumin shi ne ya aikata laifin ba tare da wata shakka ba.
Mai shari’ar ta furta cewa “za a rataye ka har sai ka mutu a matsayin hukunci kan kisan da ka yi wa Oluwabamise Ayanwola.”
Duk da cewa babu shaidun da suka yi karin haske kan yadda lamarin ya faru, kotun ta dogara da bayanai kan abubuwan da suka faru, da bayanan likita da kuma bayanan da wadda aka kashe tayi kafin mutuwarta.
Kisan Bamise a shekarar 2022 ya fusata al’umma tare da janyo tofin Allah tsine, wanda ya sanya shari’ar ta ɗauki hankalin al’umma.
Kotun ta ce direban ya yi ƙaurin suna wajen ɗiban fasinja ba bisa ƙa’ida bayan lokacin tashi aiki, inda yake kashe wutar cikin motar, ya kulle ƙofofi sannan ya aiwatar da sannan aikata ta’asa.
Kotun ta ƙara da cewa direban yakan yi wa mata masu ƙananan shekaru irin wannan ta’asa, yana dauke su zuwa inda babu wanda zai cece su, inda yakan yi musu fyaɗe.
Yakan sadu da su ba da amincewarsu ba, in ji kotu.