Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero

Asalin hoton, NLC

Bayanan hoto, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji da ya gabatar ga majalisar dokokin ƙasar domin bayar da dama kan sake yin nazari.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a yau Laraba.

Saƙon ya ce “domin samar da tsarin dimokuraɗiyya mai tabbatar da ci gaban ƙasa, dole ne mu gina tsarin tattaunawa, da bai wa masu ruwa da tsaki damar tsoma baki a harkar gina ƙasa.

“A kan haka ne muke sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta janye ƙudurin harajin da yanzu haka ke a gaban Majalisar dokoki domin bai wa duk ɓangarorin da suka dace bayar da gudumawa a kansa”.

Sanarwar ta ce ƙungiyar, ita ma za ta so ta taimaka wajen samar da kyakkyawan tsarin haraji wanda zai samu karɓuwa a tsakanin al’umma, kuma ya taimaka wajen ci gaban ƙasa.

Batun ƙudurin harajin da Tinubu ya gabatar, na daga cikin manyan sauye-sauyen da sabon shugaban ƙasar ya bijiro da su tun bayan hawa mulki a shekara ta 2023.

Sai dai ƙudurin harajin ya fuskanci turjiya daga ɓangarori da dama na ƙasar, ciki har da Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasar, da gwamnoni da kuma ƙungiyoyi.

Lamarin da ya tursasa wa Majalisar dokokin ƙasar jinkirta muhawara kan ƙudurin, yayin da shugaban ƙasar ya buƙaci ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta haɗa hannu da majalisar domin warware ɓangarorin dokar da ake ganin su ne suka haifar da taƙaddama.

Sai dai a tattaunawarsa da kafafen yaɗa labaru sa’ilin hutun ƙarshen shekara a birnin Legas, wadda ita ce ta farko tun bayan hawa kan mulki, Tinubu ya sha alwashin tabbatar da ganin sabuwar dokar harajin ta fara aiki.

By Ibrahim