Gwamnatin Kano ta fara kwashe ‘dubban’ yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar. An fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda aka samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran.
Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce “mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni.”
“Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba,” in ji Daurawa.
Shugaban na hukumar Hizba ya ce alƙaluman da suke da su sun nuna cewa akwai irin waɗannan yara masu gararamba a kan tituna sama da 5000. An tsara cewa yaran da aka kwashe za a tara su a wata cibiya, inda za a tantance su, sannan a san matakan da za a ɗauka.
Kano na daga cikin jihohin da ke da yawan al’umma a arewacin Najeriya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ke da yawan ƙananan yara waɗanda ba su zuwa makaranta.

Ko da yake jihar na daga cikin waɗanda suka sanya hannu kan dokar kare hakkin yara a Najeriya, har yanzu akwai dubban yara da ke tallace-tallace ba tare da zuwa makaranta ba, yayin da wasu yaran kuma ke barace-barace a kan tituna da sunan neman ilimin addini.
Sheikh Daurawa ya ce bayan kammala tantance yaran, zasu sanya wasu daga cikinsu makaranta yayin da za a koya wa wasu sana’a. Hakanan ya bayyana cewa akwai yiwuwar gurfanar da wasu iyayen da aka tsinci yaran nasu na gararamba kan titi a gaban kotu. “Wanda ya yi sakaci ya bar ɗansa yana yawo a kan titi duk da cewa yana da halin ɗaukar nauyinsa, to za mu gurfanar da shi a gaban kotu”.
Yaran da ba su da iyaye ko waɗanda rikici ya tarwatsa – gwamnatin za ta ɗauki matakin gyara musu rayuwa ta hanyar ba su ilimi da koya musu sana’a.