Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗu, ya nuna takaicinsa kan wasu zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdulrahman Tchiani ya yi yayin hirarsa da kafar talabijin ɗin kasar ranar Laraba.
Janar Tchiani ya zargi Najeriya da taƙaitaccen haɗin kai da kasar Faransa wajen ba ƴan bindiga mafaka da kuma ƙoƙarin kafa sansani a arewacin Najeriya, don shirya yadda za su farwa ƙasarsa.
Sai dai a hirarsa da BBC Hausa, Malam Nuhu Ribadu ya ce dukkan waɗannan maganganu basu da tushe, inda ya bayyana cewa Najeriya ba za ta taba yi wa Nijar zagon ƙasa ko ta bari wata masifa ta auku ba.
Ya ce, “Ko Ingila da ta mulki Najeriya ba ta taɓa kawo sojoojinta kasarmu ba, sai da suka yi duk wani mai yiwuwa muka ƙi yarda sannan suka kai su Nijar, ita kuma ta yadda ta karɓa.”
Ya kamata shugabannin Nijar su fahimci cewa don suna da wata matsala da Faransa, ba shi ke nufin cewa Najeriya ma ta yi zaman doya da manja da ƙasar ba.
Wani babban zargi da shugaban Nijar ya yi wa Najeriya shine na bayar da sansani ga sojojin Faransa a wani wuri a jihar Borno, inda aka ce Faransa ta jibge sojojinta a India Canada. Janar Tchiani ya haɗa sunan Nuhu Ribadu a cikin wannan magana.
A hirarsa da BBC, Nuhu Ribadu ya ce, “Ba shakka wannan shugaban Nijar ya san Najeriya sosai, amma ina roƙon ku ku je wuraren da ya faɗa ku duba da kanku, ko ku tambayi mazauna wuraren ko akwai wasu baƙi ma.”
“Ya kamata su shugabannin mulkin sojin Nijar su fahimci cewa a Najeriya ba matsala bane gare su, wannan yan ta’adda da duka muke yaki da su ne matsalarmu, ya kamata mu tunkare su tare,” in ji Malam Nuhu Ribadu.
Ya ƙara da cewa, “Don Allah shugabannin Nijar su sake dubawa, ba yadda za a yi a ce Najeriya ce za ta taimaka wa yan ta’adda su.”
“Duk wanda ya zo maka da farko zai zo a matsayin aboki ne, ko lokacin da suka kawo Faransa mun ba su wannan shawarar, amma basu ɗauka ba.”
Ya ce Najeriya ba ta da niyyar nesanta kanta da ƙasashen makwabta, domin kasashen biyu da al’umominsu yan uwan juna ne, ya kamata su haɗa kai su yi aiki tare don ci gaban juna.
A baya bayan nan, ministan harkokin wajen Nijar ya gayyaci jami’a mai kula da harkokin diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar, don ta je ta yi bayani kan zarginsa na haɗin kai da wasu kasashen Turai wajen shirya maƙarƙashiya.
Zarge zargen da shugaban Nijar ya yi wa Najeriya
Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daɗewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi.
“Wasu manyan ‘yanta’adda da muka kama, sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Najeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba da ke jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi a Najeriya sansani na horas da mayaƙan Lakurawa,” in ji shugaban na Nijar.
Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadi sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sokoto da Zamfara da jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.
Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Najeriya na sane, ba su yarda da maganar ‘yanbindigar ba.
Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da masaniya game da wannan batu.
Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabta.
Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bayar da dama ga Faransa wajen kafa sansanoni a ƙasashen domin horas da ‘yanta’adda da niyyar yaƙar Nijar.
A baya-bayan nan dai dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami, ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Najeriya da shirya maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.