Bayanan bidiyo,
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Martanin gwamnatin Najeriya kan zarge-zargen shugaban Nijar

Gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen Birgediya Janar Abdurrahamane Tchiani na haɗa baki da Faransa domin yi wa ƙasarta barazanar tsaro.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce Najeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci a Jamhuriyar Nijar.

A cikin hirarsa da BBC, Mohammed Idris ya ce Bola Tinubu, shugaban Najeriya, a matsayin shugaban ECOWAS, yana gudanar da jagoranci da ya kira ‘abin koyi’.

Ya ƙara da cewa Najeriya na martaba ƙaƙƙarfan alaƙarta da Jamhuriyar Nijar.

”Jihohin Najeriya guda takwas suna da iyaka da Nijar, don haka maganar da ya yi ba gaskiya ba ne”, in ji ministan.

”Kuma Najeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ɗorewar danganta da Jamhuriyar Nijar”, in ji Ministan.

Ministan ya ce dakarun Najeriya, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi, na samun nasara a yaƙin da suke yi da ‘yanta’adda a yankin.

”Don haka, hikima ba ta yi zargin cewa Najeriya za ta haɗa kai da wata ƙasa ta waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyata”, in ji ministan.

By Ibrahim