Kungiyar AES Sahel, da ta kunshi kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, ta sanar da samar da sabon fasfo na bai-daya ga ƙungiyar.
Sabon fasfon na ƙasashen uku zai fito ba tare da wata alama da ke alakantashi da ƙasashen mambobin kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen mambobin ƙungiyar ta ECOWAS ke tunanin yadda za su mai do da ƙasashen uku a cikin wannan kungiya.
Cikin wata hira da BBC ta yi da shi, Dr Moussa Abdoullahi, masanin diflomasiya da siyasar duniya ya ce, yanzu zirga-zirga tsakanin ƙasashen uku babu wata matsala ko shinge, to amma zirga-zirga tsakanin ƙasashen kungiyar AES Sahel da na ECOWAS, anan ne za a samu ‘yar matsala da farko.
Ya ce, “Amma dai ina ganin bai kamata ace an samu matsala ba, ko Yaya ta ke kuwa, kuma watakila ina ganin masu shiga tsakanin sabanin da ke tsakanin ƙasashen AES Sahel da na ECOWAS za su iya samun damar warware rashin matsalar a kuma sasanta ta yadda samar da fasfon ma ba za iyi wani tasiri ba.”
Masanin ya ce, “Idan har aka samu fahimta to al’ummar ƙasashen ƙungiyoyin biyu za su ci gaba da zirga zirga ba tare da wata matsala ba a kasashen duka.”
“Kaga su Kasashen ECOWAS za su iya amfani da fasfonsu su je Kasashen AES Sahel ba tare da mishkila ba, haka suma wadancan za su iya shiga ƙasashen kungiyar ECOWAS da na sau fasfon,”In ji masanin.
A watan Janairu ne ƙasashen uku dai suka fice daga ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS.
Kuma Ƙasashen na Nijar da Mali da Burkina Faso a lokuta da dama su kan nesanta kansu daga yin ƙawance da wasu ƙasashen Afirka kamar Najeriya da ma yin shelar ficewa daga ƙungiyar Ecowas sakamakon sanya musu takunkumai tun bayan yin juyin mulki a ƙasashen.
Ƙasashen dai na zargin cewa babu abin da zamansu a Ecowas ya tsinana musu, kuma yanzu dole sai Ecowas ta saurari wasu bukatun shugabannin sojin ƙasashen idan har tana son su dawo cikin ƙungiyar.
ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumai saboda kifar da gwamnatin dimokraɗiyya da suka yi.
Ecowas din ta riƙa fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane kan ta ɗage wa ƙasashen takunkuman.