Bobrisky da Very Dark Man

Asalin hoton, @verydarkblackman/@bobrisky222/Instagram

Martins Vincent Otse da mutane suka fi sani da Verydarkman ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya da aka kafa domin yin bincike kan zarge-zargen cin hanci kan wasu jami’an hukumar kula da gidajen yari da na hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa.

A kwanan nan ne Verydarkman ya yi wata fallasa inda ya saki sautin muryar da ya ce ta Bobrisky ce da ke iƙirarin biyan wasu jami’an EFCC maƙudan kuɗi domin janye wasu tuhume-tuhume da ake masa inda kuma ya yi iƙirarin cewa bai zauna a gidan yari ba tsawon hukuncin aka yanke masa.

Wannan bankaɗa ta sa hukumomi kafa kwamiti domin gudanar da bincike lamarin da ya kai ga dakatar da wasu manyan jami’an hukumar kula da gidajen yari saboda zarginsu da hannu a lamarin.

Hukumar gudanarwar kula da gidajen yari da shige da fice da gobara ta Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da jami’an ne domin ba da sararin gudanar da bincike kan zargin da ake masu.

A ranar Litinin ne Verydarkman ya bayyana gaban kwamitin inda ya yi zargin cewa Bobrisky wanda asalin sunansa Idris Okuneye yana yi wa mutumin da ake zargin ya ba shi rancen kuɗi barazana.

Verydarkman ya gabatar da jawabinsa gaban kwamitin inda kuma ya gabatar da wasu takardu da a cewarsa hujjojinsa ke nan.

Ya yi iƙirarin cewa ya yaɗa sautin muryar a shafukan sada zumunta bayan da ya saurari sautin ya kuma ga cewa wasu jami’an EFCC suna da hannu a lamarin.

A cewar Verydarkman ya yi haka ne saboda barazanar da Bobrisky ke yi wa mutumin da ya ba shi rancen naira miliyan huɗu – “mutumin ya ba shi rance kuma da lokacin karɓar rancen ya yi, Bobrisky ya ƙi biyansa, ya kuma ɓuge da yi masa barazana,”.

“Abokina ne ya aiko da rasiti, Sai Bobrisky ya riƙa roƙon abokin nawa sannan ya biya amma da na saurari sautin, sai na ajiye shi.”

Tun farko Verydarkman ya shaida wa kwamitin cewa ba zai yi magana ba matuƙar Bobrisky da shugaban EFCC Ola Olukoyede ba su bayyana gaban kwamitin ba, sai dai daga baya ya yi magana bayan da kwamitin ya nemi Verydarkman ya yi bayani kan sautin da ya yaɗa ranar 23 ga Satumba wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta.

By Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *