Asalin hoton, Atiku Abubakar
Jagoran ƴan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana ziyarar aiki da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke yi a ƙasar Faransa a matsayin ‘mummunan watsi da aikinsa’ na shugaban ƙasa yayin da ƙasar ke fama da manyan ƙalubale.
Atiku ya fitar da wannan saƙo ta hannun mai magana da yawunsa, Paul Ibe, wanda aka wallafa a shafinsa na X.
Hakan na zuwa ne yayin da ƴan adawa ke ci gaba da sukar matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na kasancewa a ƙasar Faransa duk da abubuwa na rashin tsaro da ke haifar da kashe-kashe a Najeriya.
A farkon watan Afrilu, shugaban Najeriya ya bar ƙasar zuwa Faransa domin gudanar da wata ziyarar aiki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.
Tun bayan tafiyarsa, an kai munanan hare-hare a jihar Filato, waɗanda suka yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 100.
A cikin sanarwar sa, Atiku ya tambayi “wane dalili (Tinubu) ke da shi na ci gaba da ɗaukar zango a ƙasashen Turai bayan ana zubar da jini a Najeriya?”
“Yayin da Tinubu ke cin gara a ƙasaitattun wurare, ƙasar da yake jagoranta ta faɗa tsundum cikin yamutsi,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa “idan har Tinubu na da tausayi, ya kamata ya katse tafiyarsa ya koma gida ba tare da ɓata lokaci ba.”
Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan sukar da ɗan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyarsu, Peter Obi, ya yi wa Tinubu kan tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake samun hare-haren da ke haifar da asarar rayuka a ƙasar.
A sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, a ranar biyu ga watan Afrilu, ya ce a lokcocin ziyarar Tinubu zuwa Faransa, “zai yi nazari kan ayyukan gwamnatinsa da kuma nasarorin da ya cimma.”
Haka zalika, zai yi amfani da lokacin wajen nazari kan sauye-sauyen da ya kawo sannan ya fara shirye-shirye kan bikin cikarsa shekaru biyu a cikin mulki.