Asalin hoton, FB

A makon nan ne ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta buƙaci gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da duk wasu zarge-zarge tare da sakin ɗan rajin kare hakkin bil’adama na ƙasar, Mousa Tchangari.

Tchangari na daga cikin mutane na baya-bayan nan da gwamnatin mulkin sojin ta Nijar ta kama tare da tsarewa tun bayan hawa mulki a watan Yulin 2023.

Sanarwar da Human Rights Watch ta fitar ta ce hukumomin tabbatar da ƴancin bil’adama kamar Amnesty International da World Organisation Against Torture “sun bayar da rahoto dalla-dalla kan yadda hukumomin Nijar ke taƙaita ƴancin ɗan’adam ga masu hanƙoro, ƴan jarida, ƴan adawar siyasa da kuma waɗanda ra’ayinsu ya sha bamban da na gwamnati tun bayan karɓe mulki.”

Dama dai ɗaya daga cikin fargabar ƙasashe da hukumomin duniya a duk lokacin da aka samu juyin mulki a wata ƙasa shi ne rashin tabbas game da kare ƴancin faɗin albarkacin baki da kuma haƙƙoƙin ɗan’adam.

A shekarun baya an zargi gwamnatocin mulkin soji a ƙasashe daban-daban na faɗin duniya da takura al’umma tare da hana su faɗin albarkacin baki ko kuma take musu wasu haƙƙoƙinsu na rayuwa.

Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali dai sun faɗa hannun soji bayan jerin juyin mulki da suka wanzu a ƙasashen cikin shekarun nan, wani abu da ya haifar da ruɗani na diflomasiyya a yankin yammacin Afirka tare da dagula alaƙar waɗannan ƙasashe da ƙasashen yamma.

Idan ana batun haƙƙin faɗin albarkacin baki, shin su wane ne gwamnatin Nijar ɗin ta kama tun bayan juyin mulkin watan Yulin 2023?

Ousmane Toudou, Ɗan jarida

A ranar 13 ga Afrilu, 2024, an kama Ousmane Toudou, ɗan jarida kuma tsohon mai bai wa tsohon shugaban ƙasar shawara kan harkokin sadarwa a lokacin Mohamed Bazoum da Mahamadou Issoufou.

A kwanakin da suka biyo bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023, Ousmane Toudou ya yi kira ga ɗaukacin masu rajin dimokuraɗiyya da su yi adawa da ƙwace mulkin da sojoji suka yi a cikin wani rubutu da aka yaɗa a shafukan sada zumunta.

Bayan shafe sama da wata shida ana gudanar da bincike, babban mai shigar da ƙara na kotun ɗaukaka ƙara na birnin Yamai ya buƙaci da a yi watsi da ƙarar.

Hakazalika alƙalin kotun da ke bincike na kotun soji ya bayar da umarnin soke ƙarar.

Sai dai akasin duk abin da ake tsammani, kwamishinan gwamnati ya ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.

Yanzu haka ana ci gaba da tsare Ousmane Toudou a gidan yarin Kollo da ke jihar Tillabery.

Idrissa Soumana Maiga, Editan jaridar L’Enquêteur

Idrissa Soumana Maiga

Asalin hoton, FB/Soumana Idrissa Maiga

Bayanan hoto, Idrissa Soumana Maiga

Kwanaki kaɗan kuma, a ranar 24 ga watan Afrilu, 2024, an kama daraktan buga jaridar L’Enquêteur, Idrissa Soumana Maiga, bayan jaridarsa ta buga labari kan zargin Rasha da sanya na’urorin sauraron abin da jama’a ke tattaunawa a gine-ginen gwamnatin Nijar.

Hukumomin Nijar sun ce an tsare shi ne saboda kasancewa “hatsari ga tsaron kasa”.

Sai dai Idrissa Soumana Maiga ya shaƙi iskan ƴanci a ranar 9 ga Yulin 2024.

Serge Mathurin Adou, Ɗan jarida

A tsakiyar watan Satumba, an tuhumi wani ɗan jarida ɗan asalin ƙasar Ivory Coast, Serge Mathurin Adou da ke zaune a birnin Yamai da laifin zama “hatsari ga tsaron ƙasa”.

An kama shi tare da tsare shi a gidan yari na Jamhuriyar Nijar bisa zargin yunƙurin tayar da zaune tsaye a Burkina Faso.

A ƙarshen watan Satumba, Ministan Tsaro na Burkina Faso, Mahamoudou Sana, ya zargi wannan ɗan jarida da kasancewa ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta “makirci” da kuma “ƙoƙarin da aka yi na tayar da zaune tsaye” a kan wannan ƙasa ta Sahel.

Serge Mathurin dai ya shafe watanni biyu yana tsare a asirce a hannun jami’an tsaron ƙasar ta Nijar.

Ba a samu labarinsa ba sai a ranar 13 ga watan Nuwamba ƙaramin jakadan ƙasar Ivory Coast a Yamai, Victor Akiesse, ya tabbatar da cewa Serge Mathurin Adou na raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya duk da watanni biyu da ya yi a gidan yari.

“Lallai ɗan’uwanmu yana Yamai ne kuma mahukuntan ƙasar nan sun yanke shawarar gabatar da shi gaban shari’ar ƙasar ta Nijar.

An tuhume shi da laifin yin barazana ga tsaron ƙasa, an kai shi kurkukun farar hula na Birni N’Gaouré da ke cikin jahar Dosso, inda ake cigaba da tsare shi.

Samira Sabou, mai harkar yaɗa labaru

Samira Sabou

Asalin hoton, FB/Samira Sabou

Bayanan hoto, Samira Sabou

Kamar yadda bayani ya nuna a ranar 30 ga watan Satumba 2023, wasu mutane da suka gabatar da kansu a matsayin jami’an tsaro sun kama Samira Sabou, wata yar jarida lokacin da ta kai ziyara a gidan mahaifiyarta da ke Yamai.

An ɗauki kwanaki bakwai ba a san inda Samira Sabou take ba. Da farko dai ƴansandan shari’a a birnin Yamai sun musanta kama ta, amma a ranar 7 ga watan Oktoba aka mayar da ita rundunar ƴansanda masu yaƙi da aikata laifuka ta Yamai, inda lauyanta da mijinta suka ziyarce ta.

A ranar 11 ga Oktoba, an tuhume ta da samar da watsa bayanan da ke iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a kuma an sake ta a ranar 13 ga watan Oktoban 2023.

Moussa Tchangari, Ƙungiyar farar hula

Tchangari jigo ne a kungiyoyin farar hula kuma shugaban wata babbar ƙungiya mai zaman kanta a Nijar da ake kira Alternative Espaces Citoyens.

An kama shi ne da yammacin ranar Talata, 3 ga watan Disamba, bayan dawowar sa daga wata tafiya da ya yi a ƙasar waje, kamar yadda danginsa suka sanar.

“Moussa Tchangari, sakatare-janar na kungiyar Alternative Espaces Citoyens, wasu mutane ne ɗauke da makamai suka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba ne kafin daga bisani lauyan shi ya bayyana cewa yana hannun hukumomin yaƙi da ta’addanci.”

A cikin watan Janairun 2024, cibiyar ƴan jarida ta Maison de la Presse, wata ƙungiya da ke haɗa ƙungiyoyin ƴan jaridu masu zaman kansu da na gwamnati a Nijar, hukumomin rikon kwarya sun dakatar da su tare da maye gurbinsu da wani kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida.

Ina Mohamed Bazoum da iyalansa?

Mohamed Bazoum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Bazoum

Shi dai Mohamed Bazoum da matarsa da ɗansa suna tsare ne a fadar shugaban ƙasa da ke Yamai, babban birnin kasar, tun bayan tuntsurar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Bayan shafe sama da wata biyar a tsare Kotun soji ta saki ɗan hamɓararren shugaban kasar, Salem Bazoum wanda ya bar ƙasar zuwa Togo bayan ƙoƙarin sasantawa da shugabannin yankin suka yi.

A ranar 13 ga watan Agusta, hukumomi sun bayyana aniyarsu ta gurfanar da Bazoum a gaban ƙuliya saboda “cin amanar ƙasa” da kuma yin barazana ga tsaron kasa, sai dai har yanzu ba a gabatar da shi gaban alkali ba.

Ministocin Bazoum

Baya ga Bazoum da iyalansa, hukumomin na Jamhuriyar Nijar sun kama wasu jami’an tsohuwar gwamnatin, musamman ministoci.

Cikin irin waɗannan akwai Sani Mahamadou Issoufou, tsohon ministan man fetur kuma ɗa ga tsohon shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou.

Sai Hamadou Adamou Souley, tsohon ministan harkokin cikin gida.

Kalla Moutari, tsohon ministan tsaro.

Ahmad Jidoud, tsohon ministan kuɗi.

A watan Satumba, hukumomi sun miƙa su gidajen yari na Filingué Say, Kollo da ke yankin Tillaberi, da kuma Yamai tare da gurfanar da su a gaban kotun soji da laifin yin barazana ga tsaron ƙasa.

By Ibrahim