Vampires

Asalin hoton, Getty Images

A farkon ƙarni na 18, gomman mutane a Serbia sun riƙa yin wata mutuwa mai cike da ban mamaki, inda aka yi zargin cewa maƙwafcinsu da ya mutu ne ke bibiyar su, sai su ji kamar an shaƙe su ko suna numfashi cikin wahala kafin su mutu.

Musamman wasu ƙananan kauyuka biyu, Medvedja da ke kudancin ƙasar Serbia da kuma Kisiljevo a arewa maso yammaci, nan ne aka fi samun raɗe-raɗin mutuwar.

Ƙauyukan na da nisan kilomita 200 tsakaninsu, amma sun bayar da rahotannin abubuwan ban mamaki masu kama da juna cikin shekara 10.

An aiko likitoci daga ƙasar Austria domin su binciki dalilan da suka yi sanadin mutuwar, kuma sun tattara cikakken rahoton abubuwan da suka gano.

Cikin gaggawa, rahoton bincikensu ya isa ga kafafen yaɗa labaran Austria daga baya kuma zuwa ga masu bincike a makarantu.

Masanin tarihi na Jamus, Thomas M Bohn, wanda ya wallafa littafin ‘Vampires: The Origin of the European Myth’, ya ce daga haka ne aka samo kalmar ‘Vampire’, a wata jarida mai suna ‘Wienerisches Diarium’ a shekarar 1725.

By Ibrahim