Ministocin harkokin wajen Najeriya da Nijar

Asalin hoton, Yusuf Tuggar/X

Bayanan hoto: Ministocin harkokin wajen Najeriya da Nijar

Gwamnatocin Najeriya da Nijar sun kawo ƙarshen tsamar da ke tsakaninsu tare da alƙawarin haɗa ƙarfi da ƙarfe don tunkarar matsalolin da ke addabarsu.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, wanda ya ziyarci Jamhuriyar Nijar, ya bayyana wa BBC cewa an samo bakin zaren saɓanin ƙasashen biyu.

Dangantaka ta fara taɓarɓarewa tsakanin makwabtan biyu tun bayan da sojojin Nijar suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a wani juyin mulki a 2023, tare da ci gaba da tsare shi.

A ziyarar da ministan ya kai Jamhuriyar Nijar, ya ce sun tattauna da nufin mayar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Me ƙasashen biyu suka tattauna?

Ministocin harkokin wajen Najeriya da Nijar

Asalin hoton, Amb Yusuf Maitama Tuggar/X

Bayanan hoto: Ministan wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da takwaransa na Nijar, Bakare Sankare

Ministan harkokin wajen na Najeriya ya ce batutuwan da suka tattauna sun shafi zamantakewar makwabtaka tsakanin ƙasashen biyu.

”Nijar ba za ta iya kwashe kayanta ta bar makwabtaka da Najeriya ba, haka ita ma Najeriya, tun da Allah ya haɗa mu wuri guda”, in ji shi.

Sun kuma tattauna batun tsaro tsakanin ƙasashen biyu da nufin haɗa kai don tunkarar matsalar tsaron da ke addabar ƙasashen.

”Batun tsaro abu ne da ya shafi ƙasashenmu, ba ma Nijar kawai ba har da Mali da Burkina Faso. Muna tattaunawa da su domin inganta harkokin tsaron ƙasashenmu”, in ji shi.

Ambasada Tuggar ya bayyana cewa tattaunawarsu ta amince da mayar da tsohon zama da shawarwari da ƙasashen biyu ke yi a kai a kai da aka dakatar.

”Zama ne da aka saba yi tsakanin gwamnonin jihohi da sarakunan gargajiya da ma na matakin ƙananan hukumomi na jihohin da ke makwabtaka da juna”, in ji shi.

”Irin wannan zama an daina shi, kuma a irin wannan zama ne ake tantance matakan da za a ɗauka kan abubuwan da suka danganci tsaro da kasuwanci da tattalin arziki, don haka yanzu mun amince mu maido da shi a riƙa yinsa kamar yadda aka saba a baya”, a cewar Ministan.

Haka kuma, ministan ya ce gwamnatin Najeriya ta gayyaci ministan harkokin wajen Nijar don ya ziyarci Najeriya nan ba da jimawa ba domin ci gaba da tattaunawa.

Me ya sa sai yanzu aka ƙudiri aniyar daidatawa?

Matakin daidaita alaƙar ƙasashen biyu na zuwa ne kusan shekara biyu bayan dangantakarsu ta yi tsami, sakamakon juyin mulkin watan Yulin 2023.

A tsawon wannan lokaci, dangantaka ta ci gaba da taɓarɓarewa har ta kai ga Jamhuriyar Nijar fita daga ƙungiyar Ecowas, saboda takunkuman da Ecowas ta saka wa ƙasar, sannan kuma ta fice daga ƙawancen dakarun da ke yaƙi da Boko Haram a tafkin Chadi.

Lamarin da ya sa wasu ke ganin an jinkirta yunƙurin daidaitawa tsakanin ƙasashen.

Ministan ya kare matakin da cewa ai dama dangantakar diflomasiyya ta gaji haka.

”Shi lamarin diflomasiyya, yakan ɗauki lokaci, kuma komai ana yinsa ne kan gaɓa da kuma lokaci, kuma yanzu ne lokacin ya yi, alhamdullahi an daidaita,” in ji shi.

Yaushe Nijar za ta koma cikin Ecowas?

Hoton tambarin Ecowas

Asalin hoton, Ecowas

T bayan tsamin dangantaka da ƙasashen Yammacin Afirka, Nijar ta bayyana ficewa daga ƙungiyar Ecowas tare da Mali da Burkina Faso, bayan da ƙungiyar ta riƙa matsa wa ƙasashen lamba, na mayar da su tafarkin dimokraɗiyya.

Ministan harkokin wajen na Najeriya ya ce akwai yiwuwar Nijar ɗin ta sake komawa cikin ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka.

”Ita Nijar ta nuna cewa ba ta fidda rai da dawowa ƙungiyar Ecowas ba, abubuwa suna iya canjawa kuma ta dawo cikin ƴan’uwanta,” in ji shi.

Ministan ya ce da sannu za su ci gaba da tattaunawa domin cimma hakan.

‘Yanzu komai ya daidaita’

Ministan ya ce a yanzu komai ya daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, abubuwa sun koma yadda suke a baya.

”A jawabin da ministan harkokin wajen Nijar ɗin ya gabatar ya ce a yanzu an koma zaman lafiya da so da ƙaunar juna kamar yadda ake yi a baya”, a cewar Tuggar.

A baya dai ƙasashen biyu sun kasance tamkar tagwaye, saboda dangantakar al’ada da addini da kuma kusanci da zumunci da auratayya da kasuwanci da ke tsakanin al’umomin ƙasashen biyu.

By Ibrahim