“Raguwar darajar kudin Yuan yana nuna mummunan tsammanin duniya game da dangantakar China da Amurka, bayan nasarar da Donald Trump ya samu a baya-bayan nan, da kuma wasu hasashe a kasuwannin duniya game da ci gaban kasar China,” Wang Wen, shugaban kwalejin nazarin harkokin kudi na jami’ar Renmin ta Chongyang, ya shaidawa Muryar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a ranar 15 ga watan Nuwamba, kudin yuan ko renminbi, na kara faduwa a kan dalar Amurka tun gabanin zaben Amurka da aka gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba, inda ya ragu da fiye da kashi 3 cikin dari, idan aka kwatanta da dala da aka yi a tsawon mako bakwai.

Shin Yuan zai ci gaba da faduwa har zuwa farkon shekarar 2025, lokacin da gwamnatin Trump za ta karbi ragamar mulki?

An rufe kasuwar hada-hada a ranar Talata a kan dalar Amurka 7.23, idan aka kwatanta da dala 7.09 a ranar zaben Amurka.

Wasu masana tattalin arziki sun yi imanin cewa da gangan Beijing ta ba da damar kudadenta su fadi don inganta fitar da kayyaykin China zuwa ketare. Trump ya yi alkawarin sanya harajin kashi 60 cikin 100 kan dukkan kayayyakin China.

By Ibrahim