Najeriya ta kammala wani taro na kwanaki uku domin bikin makon ma’adinai na kasa.
Mahukunta a yammacin Afirka na neman fadada zuba jari a masana’antar hakar ma’adinai a wani yunkuri na daidaita tattalin arziki, a daidai lokacin da ake fama da karuwar bukatar ma’adanai a duniya.
Taron wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da ‘yan wasa masu harkar ma’adinai da masu zuba hannun jari na kasa da kasa, wani bangare ne na kamfen da gwamnatin Najeriya ke yi na bunkasa harkar ba hako ma’adinai kawai ba, har ma da sarrafa ma’adinan da aka hako a cikin gida.
A farkon shekarar nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce za a bukaci sabbin masu zuba jari su kafa masana’antar sarrafa ma’adinai a cikin gida idan suna son samun lasisin hakar ma’adinai.