Gwamnatin Najeriya ta bada wa’adin watanni 9 ga mutanen dake boye daloli ba a cikin tsarin banki ba.

A jawabinsa ga manema labarai a jiya Alhamis bayan kammala taron Majalisar ƙolin tattalin arzikin kasar, Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce gwamnati ta bullo da wata sabuwar manufa da za ta baiwa ‘yan Najeriya damar kai ajiyar dalolinsu dake ajiye a wajen tsarin banki ba tare da an bincikesu ba.

Mr. Edun, ya ce yanzu kofa a bude take ga duk wanda zai kai kuɗaɗen sa na dalar Amurka zuwa bankuna, ba zai fuskanci wasu tuhume-tuhume ko kuma biyan haraji ba.

Edun, ya ce duk wanda ya kai kuɗaɗen zuwa bankuna, nan take za a sanya masa su a asusun da yake so, sai dai Edun ya ce idan har kudin halastattu ne.

Ministan kudin, ya kara da cewa ajiye kudaden kasashen ketare da wasu ke yi a wajen bankuna, yana daga cikin abinda ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a kasar, hakan yasa suka dauki wannan mataki da ya fara aiki ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2024.

A bayan haka dai, Ministan kudin bai bayyana irin hukunci da suka tanadar ga waɗanda suka yi burus wajen kai kuɗaɗen nasu bankuna nan da watanni 9 ba.

Shugaban masu musayar kudaden kasashen ketare Aminu Gwadabe na ganin wannan kira na gwamnatin tarayya abu ne me kyau, sai dai ya ce yanzu kudin sulalla na yanar gizo (Cryptocurrency) shi ne babban kalubale a kasar, ba wai kudaden dalar Amurka ba.

Dr. Isa Abdullahi Kashere masanin tattalin arziki dake Jami’ar Kashere a Jihar Gombe, na ganin wannan farar dabara ce Gwamnatin Tarayya ta yi, sai dai yana ganin masu ajiye da irin wannan kudade na ƙasashen ketare, ba lallai su yi mubaya’a ga wannan kira ba, saboda na tsoron tabarbarewar tattalin arzikisu.

Gwamnatin kasar dai na ta fitowa da sabbin tsare-tsare da take ganin zai iya kawowa ƴan kasar saukin matsin rayuwa da suke ciki, bayan cire tallafin Man-Fetur da tayi.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

By Ibrahim