Majalisar Wakilain Najeriya ta umarci kwamitinta kan harkokin wutar lantarki da ya binciki yawan matsalar katsewar tushen wutar lantarki na kasa sannan ya gabatar da rahoto cikin makonni uku.
Cikin mako guda, wutar lantarki ta katse akalla sau uku a duk fadin kasar yayin da ta katse sau hudu a wasu yankuna.
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin gaggawa na kasa da Hon. Mansur Manu Soro (Bauchi, PDP) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
A cikin kudurinsa, Soro ya nuna matukar damuwa kan yawan rushewar tushen wutar, wanda ya jefa kasa baki daya cikin duhu, ya kara tsananta matsalolin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Ya jaddada cewa samar da wutar lantarki mai dorewa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kowace kasa.
Ya kara da cewa a jimullance, sau takwas tushen wutar na kasa yake ruguje a shekarar 2024.