Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa ta bankado ma’aikatan bogi 6,348 yayin aikin tantance ma’aikatan da aka gudanar a jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Sagir Musa, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar yau Talata a birnin Dutse.
Ya kara da cewa rahoton aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi 6,348, tare da alkintawa jihar Naira miliyan 314 a kowane wata.
A cewar Sagir Musa, majalisar zartarwar jihar ta yi nazarin rahoton tare da kafa cibiyar cigaba da daukar bayanan ma’aikata a ofishin shugaban ma’aikatan jihar.
Ya ce, hakan zai hanzarta kammala aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da ake yi.