Kungiyar Lille ta Faransa ta doke Real Madrid da ci 1-0 a gasar Zakarun Turai ta UEFA.

Duk da Kylian Mbappé ya fito daga benci ya shiga wasan hakan bai hana Lille din mallake maki biyu na wasan ba.

A sauran wasannin da aka buga a ranar Laraba, Liverpool ta samu nasara cikin sauki akan Bologna da ci 2-0,.

Amma zakarar gasar wacce ta lashe kofin sau shida – wato Bayern Munich, ta sha kashi 1-0 a hannun Aston Villa.

Juventus, ta samu jan kati ga mai tsaron raga Michele Di Gregorio a minti na 59 amma duk da haka ta samu nasara 3-2 a kan Leipzig.

Atalanta da Feyenoord sun samu nasarar su ta farko.

Atalanta ta samu nasara da ci 3-0 kan kungiyar Shakhtar Donetsk daga Ukraine, yayin da Feyenoord ta samu nasara mai wahala 3-2 a hannun sabuwar kungiyar Girona a zagaye na biyu na wasanni.

A gefe guda kuma Benfica ta lallasa Atletico Madrid da ci 4-0 don samun nasara ta biyu a jere.

By Ibrahim