Kyaftin din kungiyar kwallon kafar Manchester United Bruno Fernandez ya tsallake hukuncin dakatarwa daga buga wasanni 3 da aka yi masa a wasan da Tottenham ta lallasa su ci 3-0 bayan da aka janye jan katin da aka ba shi.

Alkalin wasa Chris Kavanagh ne ya baiwa dan wasan tsakiyar dan asalin Portugal jan katin saboda yin keta ga James Maddison a karawar da suka yi a Lahadin data gabata a filin wasa na Old Trafford.

Manchester United Ta bayyana cewa zamewa Fernandez ya yi gabanin ya kama Maddison, wanda ya amince cewa matsalar ba ta kai a bada jan kati ba.

Yanzu dai dan wasan mai shekaru 30 na da damar karawa da kungiyoyin Aston Villa da West Ham da Brentford a wasanni 3 masu zuwa na gasar firimiya.

By Ibrahim