Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta haramtawa Samuel Eto’o shiga harkokin wasanni tsawon watanni 6 saboda wasu halaye daya nuna yayin gasar kwallon kafar mata ‘yan kasa da shekaru 20.

Tuhume-tuhumen nada nasaba da wasan Kamaru na zagaye na biyu tsakaninta da Brazil, inda kasar ta kudancin Amurka ta samu nasara da ci 3-1 bayan karin lokaci.

An baiwa Eto’o da tawagar kasar Kamaru jan kati akan bugun daga kai sai mai tsaron ragar daya baiwa Brazil damar farke kwallon da aka zura mata a wasan da suka buga a birnin Bagota, na kasar Colombia a ranar 11 ga watan Satumbar daya gabata.

An dakatar da Eto’o daga halartar wasannin Kamaru, na ajin maza ko mata, saidai dakatarwar bata shafi matsayinsa na shugabancin hukumar kwallon kafar Kamaru ta FECAFOOT ba.

By Ibrahim