An kori Bruno Fernandes daga wasa karo na biyu a jere yayin da Manchester United ta tashi 3-3 da Porto a gasar Europa League ranar Alhamis.

Dan wasan kasar Portugal din ya samu jan kati bayan aikata laifuka guda biyu da suka cancanci a hukunta shi a filin Estadio do Dragao — kwanaki kadan bayan an ba shi jan kati kai tsaye saboda wata shigar keta da ya yi a wasan da United ta sha kashi 3-0 a hannun Tottenham ranar Lahadi.

Hukuncin dakatarwar wasanni uku da aka yi masa a baya an janye shi bayan da United ta daukaka kara.

Amma an sake korar shi daga fili yayin da United ke kokarin guje wa wata rashin nasara a hannun Porto.

An kori Fernandes daga wasa a minti na 81 bayan ya samu katin gargadi na biyu saboda dagawa Nehuen Perez kafa mai tsawo wacce ta same shi.

United tana bayan Porto da ci 3-2 lokacin da aka kore shi, bayan ta fara jagoranci da ci 2-0 cikin mintuna 20 na farko.

By Ibrahim