Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya dawo gasar Premier League ta Najeriya, inda ya zura kwallaye biyu yayin da Kano Pillars ta doke Sunshine Stars na Akure da ci 2-0.

An buga wasan ne a ranar Lahadi, 6 ga Oktoba a filin wasan da kulob din ya karba na wucin gadi, inda Musa ya jagoranci kungiyar zuwa kai wag a nasara, wanda ya kawo saukin da ake bukata bayan rashin nasara a wasanni biyu a jere.

A ranar Asabar aka ruwaito cewa Musa da mai tsaron baya na Super Eagle Abdullahi Sheu sun koma kungiyar ta Pillars.

Wannan shi ne karo na uku Musa ya ke bugawa kungiyar wasa a lokuta daban-daban. Lokaci na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2021.

Musa ya gaza samun kungiya bayan da kwantiraginsa ya kare a watan Mayun 2024 da kungiyar Sivasspor.

Kano Pillars ta fara wasan cikin kuzari, inda Musa ya dauki minti hudu kacal don fara cin kwallo.

Musa ya karbi kwallon daga Mustapha Umar kafin ya buga kwallo mai karfi daga sashen 18, wanda ya sa mai tsaron ragar Sunshine Stars ya gaza iya yin wani abu.

By Ibrahim