El Rufai

Asalin hoton, OTHERS

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba zai yi gudun hijira ba duk da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ana shirin kama shi tare da azabtar da shi.

El Rufai ya bayyana haka a shafinsa na X, bayan da wani mai amfani da shafin ya wallafa cewa ya samu bayanai masu ƙarfi game da shirin kama El Rufai.

”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa da ke ofisihin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, tun watan Yulin 2024,” in ji shi.

Ya ce an aika irin waɗannan sakonnin barazanar ta hanyar abokai da ƴan uwansa, domin suna son ya ji tsoro ya yi gudun hijra da kanshi, amma El Rufai ya ce ”ba zan yi hakan ba”.

Ya ce kafin ranar 20 ga watan Fabrairu, zai dawo Najeriya, yana mai dakatar da karatun da yake yi da shirin koyon wasu harsuna, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.

El Rufai ya kuma ce kamawa da tsarewa da azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ne sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya.”

A ƴan kwanakinnan, ana ta samun ce-ce-ku-ce tsakanin tsohon gwamnan Kaduna El Rufai da ƴaƴan jam’iyya mai mulki na APC, da kuma rashin jituwa da ake zargin akwai tsakaninsa da gwamnan jihar na yanzu, Uba Sani.

By Ibrahim