Asalin hoton, Getty Images
A baya-bayan nan, hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da addabar sassan jihar Borno, wanda ke ƙara dagula zaman lafiyar al’umma da kuma ƙoƙarin gwamnatin jihar na dawo da martabar yankunan da rikicin ya shafa.
Ƙananan hukumomi da dama waɗanda a baya suka kasance cike da hada-hada sun koma wurare masu hatsari sakamakon hare-haren.
Mutanen wasu yankuna sun tsere zuwa wasu wurare, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
A ranar Lahadi, gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa sama da mutum 20,000 sun yi ƙaura daga ƙaramar hukumar Marte, sakamakon hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka tursasa wa ƙauyuka kimanin 300.
Gwamnan ya ce garin Marte wanda a kimanin shekaru huɗu da suka gabata aka dawo da al’ummarsa daga rikicin Boko Haram, yanzu ƙungiyar ta sake korar su a cikin kwana uku.
Hare-haren Boko Haram sun shafi sauran ƙananan hukumomi, kamar yadda BBC ta tuntuɓi Dr. Kabir Adamu, masani kan lamurran tsaro a yankin Sahel.
Waɗanne ƙananan hukumomi ne?
BBC ta tattauna da masu nazari kan tsaro, ciki har da Dr. Kabir Adamu da dan jarida Adamu Aliyu Ngulde, waɗanda suka lissafo ƙananan hukumomin da suka fi fuskantar hare-haren Boko Haram a shekarun baya-bayannan:
- Bama: Dr. Kabir ya bayyana Bama a matsayin wuri mafi tsanani da hare-haren Boko Haram suka taɓa a Borno. Garin ya sha fama da mamaya da ƙone-kone na dogon lokaci.
- Marte: Wannan ƙaramar hukumar ta ja hankalin al’umma a baya-bayan nan yayin da gwamnan jihar ya nuna fargaba game da yiwuwar faɗarsu hannun Boko Haram. Zulum ya ce mayaƙan Boko Haram sun tayar da sama da ƙauyuka 300 na ƙaramar hukumar.
- Konduga: “Yana ɗaya daga cikin wuraren da hare-haren Boko Haram suka yi ƙamari a kasuwanni da wuraren ibada,” in ji mai sharhin.
- Gwoza: “Wannan shi ne garin da Boko Haram ta ayyana a matsayin hedkwatarta a shekarar 2014. Duk da ƙoƙarin sojoji, har yanzu akwai yankuna da ake tsoron shiga saboda matsalolin tsaro.”
- Dikwa: Yanzu haka wannan ƙaramar hukumar ita ce ta zama mafakar ‘yan gudun hijira daga Marte da sauran garuruwa, in ji Dr. Kabir.
- Askira Uba: Mai sharhin ya ce wannan yankin tsaunuka na fuskantar matsin lamba daga ‘yan Boko Haram da ke amfani da yanayin dazuka wajen kai hari da guduwa.
- Damboa: Dr. Kabir ya bayyana cewa Damboa na daga cikin wuraren da sojoji ke yawan fafatawa da masu tayar da ƙayar baya, musamman a hanyoyin da ke kai wa yankin.
- Mafa: “Saboda kasancewarta a tsakiyar hanya tsakanin Maiduguri da Dikwa, Mafa na fama da farmaki daga ƴan Boko-Haram ɗin,” in ji Dr. Kabir.
- Jere: Dr. Kabir ya ƙara da cewa “Yana kusa da birnin Maiduguri, Jere na fuskantar barazana daga hare-haren bam da na kwanton-bauna.”
Ana kallon hare-haren Boko Haram da suka dawo a baya-bayan nan a matsayin koma-baya ga yaƙin da hukumomin Najeriya suka kwashe shekara 10 suna yi da mayaƙanta.