Daliban Jamhuriyar Nijar da ke karatu a ƙasar Rasha, sun koka tare da yin kira ga hukumomin kasar ta Jumhuriyar Nijar da su taimaka, su yi wani abu cikin gaggawa game da yanayin da su ke ciki na rashin samun allawus da kuma maganar sauyin jami’o’i da suke so su gudanar.
Mamman Kabiru Halilu Sani, shi ne mai magana da yawun kungiyar daliban jamhuriyyar ta Nijar a kasar Rasha ya kuma shaida wa BBC cewa suna cikin matsalar rashin kuɗi saboda rashin biyansu kuɗin alawus da gwamnati ke yi.
Mamman Kabiru ya ce da yawan ɗaliban na son sauya makaranta saboda tsananin sanyi da ake fama da shi a wasu yankunan Rasha, “Da yawan ɗaliban basu saba da sanyi ba, kuma basu iya karatu yadda ya kamata.”
“Wasu kuma suna fuskantar matsala ta tsadar wurin zama, shi ya sanya muka nemi jami’o’i na kirki waɗanda ya kamata yaran nan su koma, kuma jami’o’in sun amince da hakan, ma’aikata da take kula da ɗalibai ita ce za ta yi takarda.”
Mamman Kabiru ya ce sun tura takardu zuwa ga hukumomin Nijar,”Amman har yanzu abu yaƙi ci yaƙi cinye wa, akwai ɗalibai da suka yi shekara biyu da zuwa amma har yanzu ba su samu kuɗin su ba.”
“Ɗaliban Jamhuriyar Nijar dake Rasha na cikin mawuyacin hali game da rashin kuɗi, rayuwa ta yi tsada ko ina a duniya,ba kowane ɗalibi bane ake iya aikawa kuɗi daga gida, idan ba a kawo ma ɗaliban nan ɗauki ba nan gaba za su shiga cikin mawuyacin hali,” cewar Mamman
Ɗaliban sun yi kira ga hukumomin Nijar da su taimaka su kai masu ɗauki.
Dangane da waɗannan korafe-korafe da daliban suka yi, mun tuntubi Muhammed Souley, mashawarci a fadar shugaban gwamnatin mulkin soja ta CNSP a jamhuriyyar Nijar, ya kuma shaida wa BBC cewa, ɗaliban sun shiga wannan halin ne saboda sakacin gwamnatin da ta gabata.
Muhammed Souley ya ce shugaban mulkin sojin zai kai ɗauki ga ɗaliban da zarar ya samu labari, “Duk inda saƙo ya isa gare shi, shugaban ƙasa Janar Abdourrahmane Tchiani, gwamnatinmu za ta duba ta ga hanyar da za a bi a kawo sauƙi.”