- Marubuci, By Ilya Barabanov and Anastasia Lotareva
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
Shekara ɗaya ke nan tun bayan rasuwar jagoran sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, amma har yanzu babu tabbacin me ya faru da mayaƙan da kuma wasu kwantiragin da suke ciki a ƙasashen Ukraine, Syria da wasu ƙasashen Afirka. BBC Rasha ta tattauna da wasu tsofaffin sojojin Wagner, da wasu mukusantan ƙungiyar a kan halin da take ciki bayan mutuwar Prigozhin a hatsarin jirgin sama, wanda ya zo bayan yunƙurin juyin mulkin da suka yi a Rasha.
A Satumban 2023, wani matashi mai koren idanu ya tsaya a wajen duba matafiya a Babban Filin Jirgin Saman Istanbul.
Yana tsaye ne sanye da rawani a kan hanyarsa ta tafiya Libya, daga can kuma ya tafi wata ƙasar a Afirka domin neman aiki.
Ya daɗe yana aiki da mayaƙan Wagner, wanda Yevgeny Prigozhin ya ƙirkira kuma yake jagoranta.
Ƙungiyar sojojin hayan ta mallaki kamfanoni da ayyukan biliyoyin daloli, sannan ta yi aiki a Syria da Mali da kasashen tsakiyar Afirka da Sudan da Libya, sannan sojojinta ne kan gaba a yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine.
A Janairun lokacin da aka fara yaƙin, Ministan Tsaron Birtaniya ya ƙiyasta cewa akwai kusan sojojin Wagner 50,000 a Ukraine.
Amma kusa da 20,000-yawancinsu tsofaffin fursunoni-sun mutu a lokacin fafatawa domin ƙwace garin Bakhmut, kamar yadda BBC Rasha ta gani a wani jerin sunaye. Prigozhin ya janye sauran sojojinsa a Mayun 2023, inda ya zargi Ma’aikatar Tsaron Rasha da ƙarancin alburusai.
Amma sai dai mutumin wanda yake sanye da rawanin ya tsira.
Sai watan gaba aka turo masah saƙo ta Telegram cewa ana kiran sa da ya shiga cikin “zanga-zangar neman adalci.”
Yana cikin sojojin Wagner da suka ba duniya mamaki lokacin da suka kaddamar da yunƙurin juyin mulki ga Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, inda suka ƙwace birnin Rostov-on-Don a Kudancin Rasha.
Amma ƙarshen ganinsa da Prigozhin shi ne lokacin da jagoransu ɗin ya shiga mota, ya tsaya ya ɗauki hoto, sannan ya bar birnin.
Sai dai sojojin Wagner ɗin sun dakatar da zanga-zangar da suka shirya yi tun a farko. An samu matsayar ce bayan an tattauna, inda Mista Putin ya ce dole sojojin Wagner ko dai su shiga cikin sojojin Rasha ko kuma su tafi Belarus tare da Prigozhin.
Wannan ita ce matsalar, in ji matashin mai sanye da rawani, inda ya ce a lokacin ne ya gane cewa lokacin aikinsa da sojojin Wagner ya zo ƙarshe.
“Lokacin da yarjejeniyar ta fara fitowa fili, sannan akwai wasu abubuwa masu ɗaure kai, wai wasu za su tafi Belarus, wasu kuma za su tafi wasu ƙasashen, sai na yanke shawarar kama gabana,” in ji shi.
Bayan wata biyu, a ranar 23 ga Agustan 2023, wani jirgin sama mai saukar ungulu da Prigozhin ke ciki ya faɗo a Arewacin Moscow, inda ya mutu a ciki tare da wasu sojojin na Wagner.
Rasha ta yi watsi da zargin tana da hannu, amma da dama – ciki har da tsohon mayaƙin – ba su fuskanci hukunci ba.
“Lokacin da suka kashe (Prigozhin), sai ya kasance ba ni da sauran zama a Rasha,” in ji shi.
Matashin mai sanye da rawanin yana da fasfo na tafiya, wasu kuɗaɗe da kuma ƙwarewar yaƙi. Sai ya yanke shawarar tafiya zuwa Syria, inda ya taɓa zuwa yaƙi.
Majiyoyi biyu sun shaida wa BBC cewa ana ba sojojin hayan aiki tare da sojojin Rasha a Syria.
Zaɓin shi ne ko dai ka shiga aikin sojan Rasha, ko ka bar ƙasar, in ji tsohon mayaƙin.
Ba ya so ya amince da tsarin aikin, sannan ya zauna kusan wata biyu, amma an cigaba da biyansa. Sannan babu wanda ya ce masa a’a a lokacin da ya yanke shawarar tafiya Afirka aiki.
Haka kuma a lokacin shi ma Mataimakin Ministan Tsaron Rasha Yunus-Bek Yevkurov yana kan hanyarsa ta zuwa Arewacin Afirka.
Ya ziyarci ƙasashen da sojojin Wagner suka kasance suna da ƙarfi kamar su Libya da Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali, sannan daga baya ya ziyarci Nijar tare da rakiyar manyan jami’an hukumar leƙen asirin Rasha, GRU.
Kamar yadda wani rahoto da wata cibiyar ƙwararru ta Royal United Service Institute (Rusi) ta fitar, ya nuna cewa wasu tsofaffain sojojin Wagner yanzu sun fara taimaka wa wasu gwamnatocin, ciki har da masu tayar da ƙayar baya, domin a musu musaya da wasu muhimman albarkatun ƙasa.
Mali da Nijar da Burkina Faso duk sun fuskanci juyin mulki a ƴan shekarun nan-sannan suna ta ƙoƙarin janyewa daga Faransa, tare da ƙoƙarin zuwa kusa da Rasha. Bayan haka, rahotanni na nuna cewa Rasha na son albarkatun ƙasa irin su lithium da zinare da uraniun.
Haka kuma Rasha ta sanar da fara ɗaukar jami’an tsaro (Africa Corps) ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Tsaron Rasha a ƙarshen shekarar 2023.
Daga baya wannan matashin ya faɗa mana cewa ya isa wata ƙasar Afirka.
Yawancin tsofaffin abokan aikinsa sun koma aiki da Ma’aikatar Tsaron Rasha, inda yawancinsu aka kai su aiki a wani sabon ɓangaren sojin da aka buɗe.
Amma wata majiya da ke da alaƙa da Yevgeny Prigozhin ta bayyana wa BBC cewa ɗansa, Pavel yana da ƙarfin iko.
“Rasha ta ba magajinsa ƙarfin iko ya cigaba daga inda mahaifinsa ya tsaya a Afirka, a kan yarjejeniyar cewa aikinsa ba zai shafi muradun Rasha ba,” in ji majiyar.
Da farko an fara nuna yatsa a kan yiwuwar Pavel, wanda shekarunsa 20 da ƴan kai ne ko zai iya riƙe kamfanin sojojin haya na Wagner (PMC) a ƙarƙashin sunan National Guard, Rosgvardia – ba a ƙarƙashin Ma’aikatar Tsaro ba.
Rahoton na Rusi ya nuna cewa wannan ne ya sa aka yi ta kai-komo a tsakanin kwamandojin GRU da Rosgvardia.
Ma’aikatar Tsaron Birtaniya a watan Fabrairu ta bayyana cewa wasu ɓangarori uku na sojojin Wagner an haɗa su da Rosgvardia, sannan akwai yiwuwar za a tura su Ukraine ne da Afirka.
Amma har yanzu babu tabbacin hannun Pavel a harkokin sojin, sannan bai amsa neman ƙarin bayanin da BBC ta yi masa ba.
Har yanzu babu isasshen bayanin halin da sojojin Wagner suke ciki, da kuma ko wane ne yake ɗaukar nauyin su ta hanyar amfani da kafar Telegram ɗinsu, kasancewar har yanzu ana saka neman mayaƙa ta kafar domin zuwa wani aiki a wani waje mai nisa da ba a bayyana ba.
A wajen Rasha, tana amfani da Wagner ɗin ne domin cimma wasu muradunta a ƙasashen duniya.
Amma wasu tsofaffin mayaƙan Wagner suna zargi ko kuma suke nuna rashin amincewa da Ma’aikaar Tsaron Rasha.
Bayan ƙaddamar da yaƙi a Ukraine, sashen bayanan sirri na Rundunar sojin Rasha yana ta ƙara haɗa sojojin haya da suke aiki irin na Wagner.
Wani bincike da Radio Free Europe ya yi a watan Oktoba ya gano sama da ɓangarori 20 da suke aikin ɗaukar mayaƙan a ƙarƙashin Redut PMC.
Sun ƙarƙare da cewa Reduct “kamfanin soji mai zaman kansa na ƙarya ne” da yake ƙarƙashin sashen leƙen asiri na sojin Rasha GRU.
BBC ba ta samu damar tabbatar da Reduct a cikin kamfanoni masu rajista ba, sannan majiyoyi da dama sun tabbatar mana cewa kamfanin na da alaƙa da GRU da Ma’aikatar Tsaro.
Da Reduct da Rasha duk ba su amsa tambayoyin BBC ba a game da matsalar.
BBC ta zanta da wani tsohon sojan Wagner wanda ya yi aiki da ɓangaren da ake kira Medvedi – Bears – ko kuma 81st Special Operations Brigade.
A Agustan 2023, wani shafin kafofin sadarwa mai goyon bayan sojojin Rasha VKontakte ya bayyana guraben ɗaukar aiki ga Bears.
“Muna neman direbobin jirgin sama da masu gyara na AN-2 AN-2 [biplanes], MI-8 [helikwafta], and MI-24 [helikwafta mai bindigogi] kanikawa,” kamar yadda sanarwar ta fitar.
“Akwai albashi mai kyau wanda ya fara daga roubles 220,000 ($2,500) a wata da wasu alawus-alawus. Kwantiragi ne na wata shida. Ana neman masu shekara 22 ne zuwa 50. Ku zo Crimea, Simferopol. Za mu tanadar da tufafi da horo.”
Duk a rubuce an bayyana cewa masu sha’awar aikin su je Crimea ne, kafar Nomade Sahelian ta ce ƙungiyar ta kuma buɗe hedikwata a Ouagadougou, Babban Birnin Burkina Faso, sannan suna ɗaukar mayaƙa aiki na wata uku, da albashin da ke tsakanin $2,500 to $4,000.
Bisa la’akari da tattaunawar da BBC ta yi da wasu tsofffin sojojin na Wagner, BBC ta gano cewa da dama daga cikinsu suna cigaba da zama a Afirka, ciki har da Burkina Faso.
Wani wajen da ake tunanin akwai sojojin Wagner kuma shi ne Chechnya da ke Kudancin Rasha.
A Afrilu, jagoran Chechn, Ramzan Kadyrov ya ce 3,000 daga cikinsu za su shiga cikin jami’an tsaron Akhmat, kamar yadda Kamfanin Dilallancin Labaran Rasha, Tass ta bayyana.
Wani fitaccan mayakin Wagner mai suna Alexander Kuznetsov, wanda aka fi sani da “Ratibor” ya bayyana a wani bidiyo tare da Mista Kadrov, yana bayyana wa tsofaffin abokan yaƙinsa cewa, “za a cigaba da komai kamar yadda yake a lokacin Wagner. Babu wani canji.”
BBC ta samu damar tabbatar da mutum nawa daga cikin 3,000 suka iso ba.
A game da batun sojojin Wagner da za su je Belarus kuwa, yanzu haka ƙasa da 100 sun isa, inda suke horar da jami’an tsaron Shugaban Ƙasa Alexander Lukashenko.
A 28 ga Yuli, an samu rahotannin cewa akwai wani tsohon sojan Wagner a Mali, inda aka samu labarin ya mutu a harin ƙunar bakin waken da aka kai wa sojojin haya na Rasha da sojojin Mali, wanda ake zargin ƴan tayar da ƙayar bayan Tuareg da kitsawa.
Zauren Telegram na sojojin Wagner PMC ba ya bayar da isasshen bayani a kan komai, amma ya bayyana cewa an kashe wasu daga cikin sojojinsu, ciki har da kwamanda, amma ba su faɗa adadin waɗanda suka mutun ba.
Amma wani zauren Telegram mallakin magoya bayan sojojin Rasha ya bayyana cewa gomman sojojin Wagner sun mutu.
Ana zargin sojojin na haya suna cikin jami’an tsaron Africa Corps, amma da ita Ma’aikatar Tsaron Rasha duk sun ƙi cewa komai a game da hakan.
Tun wancan lokacin ba mu sake ji daga matashin mai sanye da rawani ba, amma mahaifiyarsa ta sanya kyandir na cewar ta rasa wani nata a shafukanta na kafofin sadarwa.