Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar PDP a Najeriya ya bayyana damuwarsa game da ficewar mambobinsa zuwa jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta nuna shirin samun nasara a babban zaɓen ƙasar na 2027 da ke tafe.
Wannan bayani ya fito ne daga babban taro da suka gudanar a Abuja, inda suka ce ƴan Najeriya sun gaji da halin da gwamnatin APC ta jefa su.
Taron ya biyo bayan rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta, wanda har yanzu ba a warware shi ba.
Shugaban riko na PDP, Ambasada Iliya Damagun, ya shaida wa BBC cewa sun yi Alla-wadai da ficewar mambobin jam’iyyar.
“Sun ce suna ficewa daga PDP ne saboda suna neman taimakon shugaban ƙasa don shiyyoyinsu. Na ga wannan kuskure, saboda mutumin da kowa na kukanka da shi, to da wane lokaci za ka kai kuka gida mutuwa,” in ji Damagun.
Damagun ya ce za su bi matakin shari’a domin karɓar kujerun da waɗanda suka fice suka tafi da su.
Hakanan, yawan mambobin PDP da ke ficewa zuwa APC na furyar fargaba a tsakanin jama’a game da tasirin da hakan zai yi ga manyan jam’iyyun da ke ƙalubalantar shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Damagun ya tabbatar cewa wannan ba zai ba su tsoro ba, domin masu sauya sheƙa na matakin ba daidai bane, lokacin da al’umma suka gaji da mulkin gwamnatin APC.
A cikin ‘yan kwanakin nan, an sami manyan mambobin PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da duk Ƴan majalisar jihar, da Ɗan majalisar dattijai daga jihar Kano, Sanata Adulrahman Kawu Sumaila na NNPP.