A yau juma’a ne aka cika shekara ɗaya cur da juyin mulkin sojoji wanda ya kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.
Saɓanin alwashin sojoji shugabannin ƙasar, hare-haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya ba su ragu ba, ‘yan tawaye da suka ɓullo sun tarwatsa bututun fitar da ɗanyen man fetur.
Ƙasashen duniya sun yi ta Alla-wadai da tsare hamɓararren shugaban ƙasar, wanda Tarayyar Turai ta bayyana a matsayin cin amanar ƙasa.
Ra’ayoyi sun rabu gida biyu a farkon juyin mulki, inda magoya bayan PNDS Tarayya suka gudanar da zanga-zanga, yayin da masu goyon bayan juyin mulki suka mayar da martani, inda har aka samu ƙone-ƙonen dukiya.
26 ga watan Yulin 2023, rana ce da ta hudo wa Nijar, da wani lamari mai cike da mamaki da fargaba.
Sojojin tsaron fadar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Janar Abdurrahamane Tchiani sun yi garkuwa da Mohammed Bazoum.
Tsoron da aka ji na aukuwar tashin hankali, a ƙarshe ya faɗa wa hedikwatar jam’iyyar PNDS Tarayya, inda masu goyon bayan juyin mulki suka kai farmaki, tare da ƙone-ƙonen dukiya.
An ga fuskokin murna da farin cikin zuwan sojoji a titunan biranen Niamey daga bisani. Har yanzu kuma, wasu na darawa
“Duk talakan Nijar babu wanda zai ce bai ji daɗin wannan juyin mulkin ba, saboda abubuwa da dama sun wakana, mutane sun samu albarkacin bakinsu suna faɗi,sun kuma samu jin daɗin rayuwa.”
Manyan Ƙasashen Yamma kamar Faransa da Amurka da Jamus da Rasha da Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka sun yi alla-wadai da matakin tsare Bazoum.
Ecowas har sai da ta bai wa sojojin juyin mulki wa’adi na su mayar da Bazoum kan mulki ko kuma ta tura dakaru Nijar. Ta ƙara da takunkuman karya tattalin arziƙi ciki har da rufe kan iyakokin Nijar.
Batun ya yi matuƙar taɓa rayuwar al’ummar ƙasar, wadda ta dogara da tashoshin ruwa na maƙwabtanta kamar Benin da Najeriya wajen shigar da kayan buƙatun rayuwa.
Katse lantarki daga Najeriya da rufe wasu asusun ajiyar kuɗi na Nijar da soke ratsawar jiragen sama ta sararin samaniyar ƙasar bisa fargabar kai wa ƙasar hari, sun durƙusar da harkoki da dama tsawon watanni.
Fatattakar dakarun ƙasashen waje kamar na Faransa da Amurka da ke kammala kwashe dakarunta da suka rage a sansaninta na jirage marasa matuƙa na Agadez a farkon wata mai kamawa, da ficewar sojojin Jamus, bayan jerin zanga-zanga da zaman dirshen na wasu ‘yan fafutuka, ya yi matuƙar faranta ran al’ummar Nijar.
“An samu cigaba ganin yadda al’ummar ƙasar suka tashi tsaye, suka goya wa waɗannan sojoji baya, har yau muka samu ƴancin kanmu, daga ƙasar Faransa da ta yi mana mulkin mallaka shekara da shekaru,”in ji wani ɗan ƙasar.
Wata ita ƴar Nijar din ta ce an samu cigaba sosai,”An samu cigaba da dama, ɓangaren tsaro da kiwon lafiya, ma’aikata ba a ta ɓa fashin biyansu ba, sai dai har yanzu talaka bai ji dadin da ya kamata ya ji ba.”
Sai dai kuma rashin tsaron da ƙasar ke fama da shi tun a 2012 daga masu iƙirarin jihadi a Sahel, ya daɗa ruruwa.
Hare-hare kan fararen hula da sojoji sun ta’azzara a jihar Tillaberi.
A farkon wannan wata ma, an fasa gidan yarin Koutoukale mai matuƙar tsaro, inda rahotanni ke cewa gomman fursunoni sun tsere.
Hukumomi sun ƙaƙaba dokar hana fitar dare a birnin Tillaberi.
Damar ‘yancin faɗar albarkacin baki ta yi ƙaranci, ‘yan ƙasar da dama ne ke tsoron kamu da ɗauri a duk lokacin da suka faɗi ra’ayin da bai yi wa masu mulki dadi ba.
“Ni yanzu abun da nake ganin matsalar mutanen ita ce , kamar ba ka iya fitowa ka faɗi gaskiya, ita gaskiya kowane mataki kake idan aka faɗi maka ita ana nufin ka gyara, mai faɗi amaka gaskiya ba maƙiyinka ba ne,” in ji wani ɗan ƙasar.
An kuma shiga matsin rayuwa, ga kuma hauhawar farashi. Abin da mutane suka fi ƙarfinsa a baya, yanzu ya zo ya fi ƙarfin wasu.
“Saboda Allah ɗan Nijar na cikin wani mawuyacin hali, na cikin takura, abin da muke fata Allah Ya sa kada nan gaba a faɗa cikin yunwa.”
Hukumomin Nijar dai a yanzu haka suna ƙoƙarin dawo da dangantaka da Benin, wadda alaƙarsu ta ƙara tsami a watan Mayu, bayan Benin ta hana Nijar amfani da tashar ruwanta wajen fitar da ɗanyen man fetur.
Lamarin na zuwa ne yayin da wasu ‘yan tawaye da suka ɓulla suka kai hare-hare kan babban bututun man fetur na ƙasar.
Wani abin farin ciki da ya samu Nijar shi ne kuɗi dala miliyan saba’in da ɗaya da Asusun Lamuni na Duniya ya amince da bai wa ƙasar don bunƙasa tattalin arziƙinta.
Wata sanarwa ta IMF ta ce hasashen bunƙasar tattalin arziƙin Nijar ya ƙaru saboda man fetur da ta fara fitarwa waje, da kuma cire mata takunkumai, ga kuma bunƙasar noma.
Alaƙa ta ɓaɓe tsakanin Nijar da manyan ƙawayenta na Yamma kamar Jamus da Faransa da Tarayyar Turai da Amurka.
A maimakon haka, hukumomin ƙasar sun ƙarfafa ƙawance da Rasha da Turkiyya da kuma Iran.
Matakan da hukumomi suka ɓullo da su, na ƙaddamar da shirin sayar da shinkafa mai rahusa da rage farashin litar man fetur, ba su kawo wani sauyin a-zo-a-gani ba ga rayuwar talakan Nijar.