An cika shekara ɗaya bayan da sojoji suka tuntsurar da gwamnati a ƙasar Gabon a ranar 30 ga watan Agustan 2023.
Juyin mulkin da aka yi wa shugaban na Gabon, Ali Bongo ya faru ne bayan jerin wasu juyin mulkin a ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.
Wani abu da ake wa kallon guguwar juyin mulkin da ta faɗo kan nahiyar ta Afirka bayan shekaru.
Nahiyar Afirka dai ba baƙuwa ce ga juyin mulki ba, musamman a yammaci da kuma tsakiyarta.
BBC ta tattaro muku bayani kan jerin juyin mulkin da aka samu a ƙasashen nahiyar Afirka tun daga shekarun 1950.
Karanta bayani dalla-dalla a ƙasa: