Ƙasar Faransa ta buƙaci a saki hamɓararren shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ” cikin gaggawa sannan ba tare da wani sharaɗi ba” wanda ya kwashe kimanin shekara guda a tsare tun bayan hambare shi ta hanyar juyin mulki.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta ce ” Bazaoum yana tsare na tsawon shekara guda a wani mummunan yanayi”. In ji mai magana da yawun ma’aikatar, Christophe Lemoine.
“A koyaushe muna allawadai da tsare Bazoum, za kuma mu ci gaba da sukar hakan tare da neman a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba,” kamar yadda ta shaida wa manema labarai.
Farance ta damu dangane da ƙudirin dage wa Bazoum rigar kariya da fuskantar shari’a ” wanda hakan ka iya ƙara lalata yanayin da yake ciki a tsare”, in ji Lemoine.
A 2021 ne dai aka zaɓi Bazoum a matsayin shugaban jamhuriyar ta Nijar inda kuma a watan Yulin shekarar 2023 ne sojoji ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tiani suka yi masa juyin mulki. Mohamed Bazoum dai ba yi murabus ba kuma har yanzu yana iƙrarin shi ne halastaccen shugaban ƙasar.
Ana dai zargin Mista Bazoum ne wanda yake tsare kuma aka hana ganin lauyoyinsa, da laifin barazana ga tsaron ƙasa da kuma cin amanar ƙasar.
Sojojin sun tuhume shi da kitsa amfani da “dakarun soji” domin taimakon sa wajen murkushe juyin mulki, a wata tattaunawa ta waya da shugaban Faransa, Emmanuel Macron da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken.
Gwamnatin sojin ta Nijar dai ta nei Faransa ta janye sojojinta daga ƙasar waɗanda suka kasance a jamhuriyar domin yaƙar ta’addanci a ƙarshen shekarar 2023. A watan Satumba ne kuma ake sa ran sojojin Amurka za su fice daga jamhuriyar.