Yayin da gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyar Nijar ke juya wa ƙasashen yamma baya, yanzu gwamnatin ta ƙulla wata yarjejeniyar haƙar ma’adanai mai tsoka da ƙasar Turkiyya.
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu ta ƙunshi bai wa duk wani kamfanin Turkiyya da ya nuna aniyar gudanar da aikin haƙo ma’adanai a ƙasar ta Nijar “duk abin da yake buƙata.”
An sanar da ƙulla yarjejeniyar ne a lokacin ziyarar da manyan jami’an gwamnatin Turkiyya suka kai a Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje na Turkiyya, Hakan Fidan.
Ziyarar jami’an Turkiyyar na zuwa ne watanni bayan ziyarara da Firaiministan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahamane Zeine ya kai Turkiyya.
Hukumomin Nijar sun ce ziyarar da jami’an Turkiyya suka kawo a ƙasar, ɗorawa ne kan alaƙar da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu a ziyarar da Firaiministan Nijar ya kai a watannin baya.
Mene ne yarjejeniyar haƙar ma’adanan ta ƙunsa?
“Muna sa ran cewa masu saka jari a ɓangaren tattalin arziƙi za su zo domin zuba jari a Nijar, kuma za mu ba su duk abubuwan da suke buƙata ta yadda al’ummarmu za su ci gajiyar ma’adanan da za a haƙo,” kamar yadda aka ambato Firaiministan Nijar, Ali Lamine Zein na bayyanawa a lokacin ganawarsa da tawagar gwamnatin Turkiyya.
Ƙungiyar ƙasashe masu samar da makamashin nukiliya ta ce Nijar ce ƙasa ta bakwai cikin ƙasashen da ke samar da makamashin uranium.
Nijar na daga cikin ƙasashe na gaba-gaba da ke samar da makamashin uranium ga ƙasashen nahiyar Turai, waɗand ke amfani da shi wajen samar da makamashi.
Kafin wannan lokaci, Faransa ce babbar mai ruwa da tsaki a harkar makashin uranium na Jamhuriyar Nijar.
To amma tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yunin bara, ƙasar ta riƙa juya wa ƙasashen Yamma baya, kuma ta katse hulɗoɗin tattalin arziƙi da dama da su.
Wannan ya haɗa da ƙwace lasisin haƙar ma’adanai na kamfanin haƙar ma’adanai na Orano na Faramsa.
Kamfanin ya kwashe sama da shekara 40 yana aiki a Nijar, har ma ya fara shirin ƙaddamar da ɓangare na uku na ayyukan haƙara ma’adanai a wurin haƙar ma’adanai na Imouraren, wanda shi ne wuri mafi arziƙin uranium a ƙasar.
Haka nan a farkon wannan wata ne shi ma kamfanin haƙar ma’adanai na ƙasar Canada, GoviEx ya rasa nasa lasisin haƙar ma’adanan a ƙasar.
Waɗanne ƙasashe ne kuma ke kwaɗayin albarkatun ƙasa na Nijar?
Yayin da Jamhuriyar Nijar ke neman ƙulla alaƙa da sabbin ƙawaye, ƙasashe da dama na gogoriyo wajen ganin sun mamaye harkar haƙar ma’adanai ta ƙasar.
“Ba Turkiyya ce kaɗai take ƙwallafa rai kan makamashin uranium na Nijar ba, Iran ma ta je, sannan Nijar ɗin ta ƙulla yarjejeniya da Rasha kan ma’adanai domin taimaka mata wajen samar da makamashi” in ji Sam Murunga, wani mai yi wa BBC sharhi kan lamurran Afirka.
Waɗannan ƙasashe na neman cin gajiya da dama. Turkiyya, wadda ta daɗe da burin ganin ta samar da makamashi ta hanyar nukiliya, tana son ta yi amfani da wannan dama wajen cimma burinta.
“Turkiyya na neman cin gajiyar wannan lokaci da Nijar ke neman sabbin ƙawaye, ita kuma Nijar na ganin cewa a shirye take ta ƙulla alaƙa da duk wata ƙasa wadda ba Faransa ko Amurka ko ƙasashen Turai ba ne, wadda za ta ce tana son ta ba ta taimako a harkar tsaro da kariya daga maƙiya,” in ji Mista Murunga.
Waɗanne yarjejeniyoyi Nijar ta ƙulla?
Baya ga Rasha, Jamhuriyar Nijar na ganin cewa za ta iya kulla yarjejeniya da Turkiyya a bangaren tsaro, domin ganin ta yaki mayakan kungiyar IS da na Alqaeda wadanda ke addabar yankin Sahel.
“Mun tattauna kan yadda za mu bunkasa bangaren tsaro da tattara bayanan sirri a kokarin da ake yi na yaki da ta’addanci a Nijar, kamar yadda muka yi a Somaliya,” in ji ministan harkokin waje na Turkiyya, Hakan Fidan.
A watan Afrilu, Turkiyya da Jamhuriyar Nijar sun amince da su kara karfafa dangantaka ta tsaro ta hanyar samar da jirage marasa matuka kirar Bayraktar TB2 ga rundunar sojin Jamhuriyar Nijar. Haka nan kuma Turkiyya za ta bai wa Nijar makaman da hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum ya yi oda daga kasar.
A lokaci daya duk wasu yarjeniyoyin da Nijar din ta kulla da kasashen Yamma sun wargaje.
A watan Maris, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da Amurka, inda hakan ya tursasa wa dakarun Amurka masu yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel ficewa daga kasar.
Gwamnatin sojin ta Nijar ta bai wa Amurka wa’adin zuwa tsakiyar watan Satumba ta gama kwashe daukacin dakarunta daga kasar.
An ruwaito cewa tuni wasu dakaru daga Rasha suka fara maye gurbin sojojin Amurka a sansanonin da suka riga suka bari.
Jim kadan bayan aiwatar da juyin mulkin ne kuma aka kori sojojin Faransa, wadanda suka je kasar domin yaki da masu ikirarin jihadi.
Alaƙar Turkiyya da nahiyar Afirka
Turkiyya ta bai wa kanta wani matsayi na mai son kulla alaka da kasashen Afirka ta fannin kasuwanci da tsaro da ci gaban kasashe.
Ta na ikirarin zama zabi mafi dacewa ga kasashen na Afirka, wadda ba ta zo da nufin “mulkin mallaka” ba.
Kuma ta ci gaba da kafa kanta a nahiyar ta hanyar bude ofisoshin jakadanci 40 tare da kulla yarjeniyoyin habbaka tattalin arziki da kasashen Afirka 48, kamar yadda alkaluma na ma’aikatar kasuwanci ta Turkiyya suka nuna.
Alaka ta soji na daga cikin abubuwan da ke kara habbaka wannan dangantaka.
Cibiyar sojin Turkiyya mafi girma a wani wuri wanda ba kasar ba yana a Somaliya ne, kuma Turkiyya na bai wa sojojin Somaliya horo.
Haka nan kuma kasar na sayar da makamai ga kasashen Afirka akalla guda 14, ciki har da Mali da Burkina Faso da Togo da kuma Jamhuriyar Nijar wadanda ke amfani da jirage marasa matuka kirar Turkiyya domin yaki da ‘yan bindiga a yankin.