Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tchiani ya haramta wa wasu ƴan ƙasar mutum tara ayyana kan su a matsayin ƴan jamhuriyar Nijar, bayan da ya ƙwace shaidar zamansu ƴan ƙasar.
A Wata sanarwa da aka watsa a gidan talbijin ɗin ƙasar wadda shugaba Tchiani ya saka wa hannu, ta fitar da jerin sunayen mutanen da abin ya shafa da suka haɗa da tsohon ministan ma’aikatar yawon buɗe idon ƙasar,Rhissa Ag Boula, da Ighazer Hamidine Abdou.
Gwamnatin dai ta zarge su da aikata ta’addanci da cin amanar ƙasa da karya dokokin ƙasa.
A watan Agusta ne Janar Tchiani ya sanya wa dokar korar duk wani ɗan Nijar da aka samu da hannu wajen cin amanar ƙasar rigar kasancewarsa ɗan jamhuriyar wadda ta janyo ka-ce-na-ce ciki da wajen ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta ce dokar wani salo ne na tauye haƙƙin ƴan ƙasar.
Hakan na nufin yanzu dai mutanen da aka kora din ba su da wata ƙasa da za bayyana a matsayin ƙasarsu.
Babu cikakken bayani dai na halin da mutanen da aka korar suke ciki.
Mutanen tara sun zamo na farko da aka ƙwacewa shaidar zamansu ƴan ƙasar tun bayan fito da dokar a watan Agusta da masana suka ce wani yunƙuri ne na toshe bakin masu hamayya.
Akwai alamun da ke nuna cewa akwai yiwuwar za a kama mutanen tara sannan a gwamnatin sojan za ta yanke musu hukunci tunda a yanzu haka suna matsayin waɗanda ba su da ƙasa.
Har yanzu dai gwamnatin sojin ta Nijar na ci gaba da tsare hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.