Ra’ayi Riga: Kan cikar Ecowas shekara 50 da kafuwa

Shirinmu Ra’ayi Riga na wannan makon ya tattauna kan cikar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas ko kuma Cedeao), shekara 50 da kafuwa.

An kafa ƙungiyar ne ranar 28 ga watan Mayun 1975 da burin haɗa kan ƙasashen Afirka ta Yamma.

Babbar manufar Ecowas ita ce inganta haɗin gwiwar ƙasashen kan harkokin tattalin arziƙi, da nufin haɓaka matsayin rayuwar al’ummomin Afirka ta Yamma da bunƙasa ci gaban tattalin arziƙi, da ƙara danƙon alaƙa tsakanin ƙasashen yankin.

Cikar Ecowas shekara 50 da kafuwa na zuwa daidai lokacin da ƙungiyar ke fama da ɗaya daga cikin mafi girman ƙalubale da ya taso mata, wanda ya shafi fitar mambobinta uku: Nijar, Mali da Burkina Faso, ƙasashen da suka kafa wata sabuwar ƙungiya bayan sojoji sun yi juyin mulki.

By Ibrahim