Bola Tinubu

Asalin hoton,
Nigeria State House


Bayanan hoto,
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, shi ne shugaban majalisar shugabannin ƙasashe na Ecowas

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta buƙaci ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da suka fice daga cikinta da su fice gaba ɗaya daga dukkan hukumominta da cibiyoyinta da suke ciki.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci ƙasashen da su miƙa cibiyoyinta da ke cikin kasashensu, tana mai cewa dukkanin ‘yan ƙasashen uku da ke aiki a hukumominta za su bar ayyukansu.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron ministocin harkokin waje na mambobinta da aka gudanar a wannan makon a ƙasar Ghana.

A ƙarshen watan Janairu ne ƙasashen uku da ke ƙarƙashin mulkin soji suka kammala ficewa daga Ecowas a hukumance bayan sama da shekara guda ana tattauna.

Ficewarsu ba ƙaramin abu ba ne ga Ecowas, wadda a shekara 50 da suka gabata ake yi wa kallon ƙungiya mafi girma da tasiri a yankin.

An fara musayar yawu ne bayan ƙasashen uku sun ƙi amincewa da komawa mulkin dimokuraɗiyya, kuma tuni suka kafa tasu gamayyar mai suna Alliance of Sahel States (AES).

Ƙungiyar mai mambobi 15 ta ce za ta bar “ƙofarta a buɗe” ga ƙasashen uku, idan suka yanke shawarar komawa cikinta.

‘Rasa ayyuka’

Yusuf Maitama Tuggar

Asalin hoton,
@YusufTuggar


Bayanan hoto,
Ministan Harkokin Waje na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar, shi ne ya jagoranci taron ministocin na Ecowas a Ghana

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar yana cikin mahalarta taron na Ghana, kuma ya faɗa wa BBC wasu daga cikin muhimman hukumomi da cibiyoyin da ƙasashen ke ciki na Ecowas waɗanda yanzu ake so su fita.

“Akwai babbar hukumar kiyaye lafiya da ke Burkina Faso, wannan hukumar za ta tattara kayanta ta koma wata ƙasa da ke cikin Ecowas tun da Burkina Faso ta fice daga ƙungiyar,” in ji ministan.

“Akwai kuma babban ofishi na kula da harkokin kuɗaɗe domin tabbatar da cewa ana bin doka wajen sarrafa kuɗaɗe da hana safarar miyagun ƙwayoyi.”

Ministan ya kuma ambaci wasu manyan ofisoshi da ke kula da kiwon lafiyar dabbobi da hanyoyi da tituna da kuma aikin bututun gas a yankin Ecowas, inda ya ce duk za a warware komai da ƙasashe ukun da suka fice.

“Ma’aikatan ƙasashen uku da ke aiki a hukumomin Ecowas za su rasa ayyukansu gaba ɗaya saboda duka su ma za su fice.”

A cewarsa: “Kazalika, akwai bankin Ecowas da ya zuba jari fiye da dala miliyan 280 a ayyuka daban-daban a ƙasashen. Da zarar ƙasashen sun fita daga ƙungiyar, za a fitar da dukkan ma’aikatan bankin da ke can.”

Ya jaddada cewa akwai ƙa’idoji da dokokin Ecowas da za a bi cikin lumana wajen warware dukkanin al’amuran da suka shafi rabuwar.

A shekarar da ta gabata, shugabannin Ecowas suka sanar da ƙarin wa’adin wata shida ga ƙasashen na Nijar da Mali da Burkina domin su sake tunani kan ficewarsu, amma hakan bai yiwu ba.

By Ibrahim