Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Bayanan hoto,
Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi a lokacin da ya kai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu ziyara a makon da ya gabata
Sanatocin Najeriya uku daga jihar Kebbi, waɗanda suka wuce daga PDP zuwa APC sun ce sun fice daga jam’iyyar saboda rikice-rikicen cikin gida.
A jiya Talata, shugabancin majalisar dattijai ya tabbatar da sauya shekar sanatocin: Sanata Adamu Aliero, Yahaya Abdullahi, da Garba Maidoki.
Sanatocin sun bayyana cewa sun fice daga PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar.
Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa a bayyane take cewa tun bayan zaɓen 2023, PDP ta shiga ruɗani da rikici.
Ya ce, “Kowa ya san abinda ya addabi PDP, tana son ta wargaje. Dukkan ‘yan jam’iyyar suna rarrabuwa.”
Sanatan ya bayyana cewa sun fice daga APC a baya saboda gwamnan su na lokacin, amma yanzu sun koma.
Yahaya Abdullahi ya musanta cewa akwai alƙawari daga Tinubu kafin su sauya sheƙa zuwa APC, yana mai cewa ya wuce lokacin alƙawari.