Sansanin Al Udeid, wanda ke wajen Doha, babban birnin Qatar, cibiyar rundunar sojin sama Amurka ce a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan sansanin na ɗauke da dakarun Amurka kusan 8,000.

Har ila yau, akwai sojojin Birtaniya a cikin sansanin, wanda a wasu lokuta ake kiransa filin jirgin saman Abu Nakhla.

Cibiyar ta zama shalkwatar shirya dabarun yaƙin sojojin Amurka masu aiki a Iraƙi da sauran ƙasashen yankin Gulf.

A shekarar 2000, Qatar ta bai wa Amurka iko da cibiyar Al Udeid.

Bayan Amurka ta karɓe ragamar sansanin a 2001, Qatar da Amurka suka amince da wata yarjejeniya a 2002, wadda ta tabbatar da zaman sojojin Amurka a Al Udeid.

A shekarar 2024, kafar yaɗa labaran Amurka ta CNN ta cimma wata yarjejeniya da ta amince da tsawaita zaman dakarun Amurka a Qatar na tsawon shekara 10.

By Ibrahim