A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Jos, babban birnin jihar Filato, ta kama wasu ‘yan kasar Sin huɗu da laifin hada-hadar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da yanke masu hukunci ɗaurin shekara 20 a gidan maza.
Wadannan ‘yan kasar Sin sun hada da Yian Quin Yong (Liang Quin Yong), Wan Hwajii (Wang Huajie), Zyon Jiyajin (Zhong Jiajing), da Long Kechong (Long Kechong). Kotun ta yanke wa kowannensu hukuncin daurin shekara biyar-biyar ko kuma zabin biyan tarar kudi naira miliyan dai-dai.
An samu su da laifin sayen ma’adinai ba bisa doka ba a ranar tara ga watan Maris a yankin birnin Jos na jihar Filato.
Babbar kotun tarayyar ta bayar da umarnin a fitar da su daga Najeriya tare da haramta masu sake shigowa kasar.
Haka zalika, kotun ta bayar da umarnin karbe dukkan ma’adinan da aka gano a lokacin gudanar da bincike da kuma tsabar kudi naira miliyan goma sha shida da dubu dari uku a matsayin tara, saboda kin bayyana harkar kudi cikin kwanaki bakwai ga sashe na musamman da ke aikin dakile hada-hadar haram a Najeriya.
Hukunce-hukunce sun biyo bayan amsa laifukan da wadanda aka tuhuma suka yi, kuma kotun ta gamsu da bayanan da aka gabatar a kan tuhume-tuhumen da aka yi musu.