- Marubuci, Armand Mouko Boudombo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Dakar
Manufar a bayyane take, game da abin da aka tattauna a baya-bayan nan cikin watan Yuli tsakanin jami’an gwamnatin Chadi da na Jamhuriyar Nijar, lokacin da ministan harkokin man fetur da haƙar ma’adanai na Chadi ya ziyarci Nijar.
Ƙasashen biyu na son “aiwatar da aikin ba tare da ɓata lokaci ba”. Ziyarar da ministan ya kai Nijar na zuwa ne bayan amincewar da Chadi ta yi game da aikin a cikin watan Mayu a lokacin wani taron ministoci.
Bututun zai haɗa da wurin haƙo man fetur na Agadem da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Nijar da yankin haƙar ma’adanai na Doba a kudancin Chadi.
Bututun da za a shimfiɗa zai shafe nisan kilomita 985, wanda zai kai man fetur zuwa wani bututun da aka shimfiɗa tun shekarar 2003, wanda zai haɗa zuwa yankin Kome a kudancin ƙasar Kamaru, shi kuma yana da nisan kilomita 1,070.
Wannan dogon zagaye za a yi shi ne domin kauce wa rashin jituwa da ake samu tsakanin Jamhuriyar Nijar da ƙasar Benin, wanda har yanzu ake ƙoƙarin yin sulhu.
A watan Maris ɗin shekarar 2024 ne Jamhuriyar Nijar ta kammala shimfiɗa bututu mai nisan kimanin kilomita 2,000 wanda zai taimaka mata wajen fitar da man fetur ta tashar jirgin ruwa da ke Cotonou.
Rashin jituwar da aka samu tsakanin ƙasashen biyu ne ya sanya har yanzu aka kasa fara amfani da bututun yadda ya kamata, wanda ya sa har ƙasar ta Nijar ke shawarar watsar da aikin da samar da wani sabo.
Ƙalubalen tsaro
Batun tura man fetur ɗinta ta ƙasar Chadi zuwa Kudancin Kamaru wata shawara da Nijar ɗin ta fara tunanin yi tun asali. Kuma ita ce ma asalin shawarar da Nijar ɗin ta fara aiwatarwa.
Ya zuwa yan dai babu ƙarin bayani kan kudin da aikin zai laƙume da kuma inda aka kwana kan aikin.
“Ba za mu ce komai ba a kansa tukuna” in ji ma’aikatar man fetur ta Jamhuriyar Nijar.
A ɓangaren hukumomin ƙasar Chadi, sun faɗa mana cewa “an riga an kammala shirye-shiryen fara aikin kuma har ma an tsara yadda aikin zai gudana”, tare da sanya hannun manyan jami’an gwamnati.
To sai dai idan aka duba wasu ɓangarorin za a ga cewa akwai babban ƙalubale da Nijar za ta fuskanta wajen aiwatar da aikin.
Rashin tsaro na daga cikin manyan matsaloli.
Yayin da yankin Agadem, inda filayen haƙo man fetur ɗin suke, ke samun kariyar jami’an tsaro mai yawa (sojoji 700), duk da haka sun yi ƙaranci, kuma ba za su iya kare tsawon kilomitocin da bututun zai shafe ba, wanda ke fuskantar barazana daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
CNPP, wanda shi ne kamfanin ƙasar China da ke jagorantar aikin haƙo man fetur a Nijar, a ranar Lahadi, 21 ga watan Yulin 2024 ya sanar da cewa zai “jingine duk wani aikin kafa kayan aiki a yankin Agadem har sai tsaro ya inganta a yankin”, bisa la’akari hare-haren da aka kai kan kamfanin tun daga ranar 12 ga watan Yuni.
Ƙalubalen zai fi ƙamari ne idan aka fara aikin shimfiɗa bututun man ta gabashin ƙasar, wurin da bai da nisa da kan iyakar Najeriya, inda ya yi ƙaurin suna wajen hare-haren ƙungiyar Boko Haram.
Rikicin Boko Haram ne ya sanya tun farko Jamhuriyar Nijar ta watsa da shirinta na tura man fetur ɗinta ta Chadi.
Kuma har yanzu “matsalar tsaron na nan yadda take, babu sauƙi”, in ji Cedik Abba, wani masanin tsaro a yankin Sahel.
Mawallafin littafin Voyage au cœur de Boko Haram (Tafiya zuwa ƙoƙuwar Boko Haram) ya ce mayaƙan Boko Haram sun farfado a cikin watannin baya-bayan nan.
Har yanzu ƙungiyar na kai hare-hare a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya, wadda ke iyaka da Diffa, yankin da filayen haƙar ma’adanai na Agadem suke, inda kuma ke maƙwaftaka da tafkin Chadi, kuma hakan zai kawo ƙalubale ga aikin matuƙar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.
Shin Nijar na da halin shimfiɗa bututun man fetur da kanta?
Ya zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana kuɗin da za a kashe ba wajen shimfiɗa bututun.
Sai dai tun asali, a lokacin da Nijar ta ke shawarar shimfiɗa bututun kafin ta sauya ra’ayi, an tsara cewa aikin zai lashe kuɗi kimanin dala biliyan hudu.
Zunzurutun bututun zai laƙume kimanin dala biliyan biyu, ko kuma 1,200 CFA, yayin da za a kashe dala biliyan 2.5 wajen samar da sauran kayayyaki da za saka, kamar yadda tsohon ministan man fetur, Foumakoye Gado ya bayyana wa manema labarai.
Babban ƙalubalen shi ne samo wanda zai zuba waɗannan kuɗaɗe domin gudanar da aikin.
China ce ta ɗauki nauyin aikin shimfiɗa bututun da ya haɗa Agadem zuwa Seme-Kpodji, wanda ya lashe kudi biliyan 2,400. Ana buƙatar kimanin rabin waɗannan kuɗaɗe wajen shimfiɗa sabon bututun da zai kai Chadi.
Ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar ba su tabbatar kan ko ko za su yi amfani da kuɗinsu ne wajen shimfiɗa bututun ba, ko ta hanyar bashi, ko kuma yin haɗaka da ƴan kasuwa ba.
Hukumomin kudi na duniya kamar Hukumar bayar da lamuni (IMF) sun bayyana cewa Nijar ba ta cika wa kanta bashi da yawa ba, kuma ta yi ƙoƙarin wajen rage kuɗaɗen da ake bin ta da kimanin ƙasa da kashi 50 cikin ɗari na tattalin arziƙinta na cikin gida.
Man fetur na daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban ta wanda zai sa ta samu bunƙasar tattalin arziƙi. Sai dai fitar da man fetur ɗin na tafiyar hawainiya tun daga farkon wannan shekara sanadiyyar tsamin dangantaka tsakaninta da Benin.
Wannan na da haɗarin ƙara girman giɓi a kasafin kuɗin ƙasar da kimanin kashi 34 cikin ɗari.
Wannan ya nuna cewa tabbas babu yadda za a yi ƙasar ta iya amfani da kuɗinta wajen aiwatar da shirin kasancewar babu isassun kuɗi a lalitarta.
Za ta iya ciyo bashi?
Wannan ne zaɓi na biyu ga ƙasar. Kasancewar ba ta da kudi na ƙashin kanta da za ta aiwatar da shirin, dole ne sai dai ƙasar ta dogara da ƙawayenta wajen samun kuɗin aiwatar da shi.
A nan ma babu haske. A kwanan nan ne ƙasar ta karɓi lamuni daga Hukumar lamuni ta IMF na kuɗi CFA biliyan 42 wanda za ta yi amfani da su a kan muhalli da kuma tallafa wa tattalin arziƙi.
Lokacin da za a ba ta kudin, IMF ta ce juyin mulkin soji da rikicin diflomasiyya ya yi wa ƙasar illa tun bayan juyin mulkin na shekarar 2023.
Duk da cewa Hukumar ta amince cewa ƙasar ta samu sauƙi sanadiyyar ɗage takunkuman da Ecowas ta yi, ta ce wajibi ne ƙasar ta nemo wasu hanyoyin samun basuka masu sauƙi.
A watan Afrilun da ya gabata ne Nijar ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba ta tsabar kuɗi dala miliyan 400 (kimanin CFA biliyan 240) da kamfanin man fetur na China (CNPC).
Ƙasar za ta biya wannan bashi ne daga cikin cinikin man fetur, musamman ta hanyar fitar da man fetur ɗin ta ƙasar Benin tare da kudin ruwa na kashi bakwai cikin ɗari – wanda masana ke ganin ya yi yawa.
A bara ƙasar ta fuskanci ƙalubalen samun kuɗi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, inda ta kasa biyan kuɗi kimanin dala biliyan 500 da aka bin ta.
Ko bututun Chadi zuwa Kamru zai ɗauke man fetur ɗin Nijar?
Ana sa ran cewa filayen haƙar man fetur na Agadem za su iya samar da ɗanyen man fetur ganga 90,000 a rana daga lokacin da aka buɗe wurin, amma zai ƙaru zuwa ganga 200,000 a rana nan da shekarar 2026.
Ana sa ran haɗa bututunda zai ɗauki ɗanyen man zuwa bututun man fetur na filayen haƙar man fetur da ke Doba a Chadi, wanda ke ɗaukar man fetur ɗin Chadi zuwa warin haƙar man fetur na Kome da ke kudancin Kamaru.
Bututun wanda aka samara a 2003 yana iya ɗaukar ɗanyen man fetur gangan 225,000 a rana. A shekarun baya-bayan nan yawan man fetur ɗin da Chadi ke haƙowa ya yi ƙasa saosai.
A cikin shekaru biyu da suka an iya haƙo gangar man fetur kimanin 140,000 a rana.
Iadan aka haɗa ganga 90,000 da Nijar ke fitarwa a kowace rana da wanda Chadi kje fitarwa za a ga cewa ana neman ƙure abin da bututun ke iya ɗauka zuwa Kamaru.
Hakan ba tare ma da an yi la’akari ke nan da ƙarin man fetur ɗin da za a riƙa haƙowa a yankin Agadem ba, wanda ake sa ran zai nunka a cikin shekara biyu.