Shakka babu akwai yankunan da ke iyakoki tsakanin Najeriya da makwabciyarta Nijar da masu riƙe da makamai ke shige da fice ba tare da wata fargaba ba.
Masana sun ce mafi yawan rikece-rikicen da ke faruwa a yankin arewacin ƙasar na faruwa ne a jihohin da ke kusa da kan iyakoki.
Rikicin Boko Haram da ake yi a yankin Arewa mas Gabas, yankin na da iyaka da Chadi da Nijar da kuma Kamaru.
A yankin Arewa maso Yamma yankin na da iyaka da Nijar, wadda iyakar ta kai girman kilomita 1,497, kwatan kwacin mil 930.
Waje ne mai girman gaske da turawan mulkin mallaka suka iyakance shi cikin shekrun 1890 zuwa farkon shekarun 1900.
Yankin yana da nau’in yanayi ya kusa biyar, akwai duhuwa inda dazuka ne cike da bishiyoyi.
Akwai inda cike yake da hamada. Sai kuma inda kwazazzabai suka cika shi.
Ka zalika hanyar da ake bi ta yankuna mafi girma na kan iyakar ba su da kyau, wani abu da ke hana kai wa ga inda aka nufa cikin sauri.
Idan kuma muka faɗaɗa bayanai a yankin Sahel za ka ga sauran ƙasashen ma suna fama da matsalar kan iyakoki.
Nijar da Mali da Burkina Faso su ma rikicin masu iƙirarin jihadi da suke fama da shi a kan iyakokinsu ne.
Iyakar Mozambique da Tanzaniya da ke fama da kungiyar ISM, suma rikicin ya fi ƙarfi kan iyakokinsu.
Da haka wataƙila mai karatu ya iya gano ƙalubalen da ke tattare da kare iyakokin ƙasashe a wajen gwamnatoci.
BBC ta tuntubi wasu masana harkokin tsaro domin jin ta yaya Najeriya za ta iya inganta tsaro a tsakanin iyakokinta da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.
DR Audu Bulama Bukarti mai nazari kan harkokin tsaro a yankin Sahel da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin tsaro na Beacon Cunsulting na da mabambantan ra’ayi kan wannan batu.
Abin da ya janyo taɓarɓarewar tsaro kan iyakar Najeriya da Nijar
Watakila daga yadda shimfidar wannan labari ta gabata mai karatu zai san akwai wuya sha’anin tsaron kan iyaka.
Amma akwai wasu abubuwa da idan aka same su za su iya inganta tsaron har su samar da kwanciyar hankali ga hukumomi da ‘yan ƙasa baki ɗaya.
- Ƙungiyoyin ‘yan bindigar nan da masu ikirarin jihadi sun kwana da sanin irin waɗannan ƙalubale da ƙasashe ke fuskanta a kan iyakoki, shi yasa suke amfani da su wajen kutsensu.
“Lakurawa da duka ‘yan bindigar da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kwana da cewa wasu ‘yankunan kan iyakar tamkar ba su san da gwamnati a wuraren ba,” in Dr Bukarti.
“Yanayin iyakar da ta tattara dazuka da hamada da kuma kwazazzabai kan mayar da hannun agogo baya a aikin ba da tsaro na wurin.
“Wani abu da yake ƙara samar da matsalar tsaro a iyakar Najeriya da Nijar shi ne, jami’an da ke kare iyakokin ba su da cikakken tsarin da suke buƙata. Jami’an kula da shige da fice da na hana fasaƙaurin da suke kan aikin kwarewarsu wajen makamai ba ta kai ta ‘yan sanda ba, ga shi ba su da isassun makaman.
“Kullum ake maganar tsaro a Najeriya babu mai magana a kan waɗannan jami’an sai dai sojoji kawai, don haka wannan ma zai iya kashe musu gwiwa,” in ji Bukarti.
Ya ce gazawarsu a kan aikinsu ce ta ja ake samun shigar makamai da kuma muggan kwayoyi da ‘yan bindigar ke ta’ammali da su. Hatta baburan da wasu jihohi suka haramta amfani da su ta nan ne ake shigo da su.
- Mayakan ƙungiyoyin jihadi na duniya suna kafa sansanoni a wasu daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya
Wannan ya samo asali ne da rashin hanyoyi a wannan yankin wadanda za a kai wuraren da masu iƙirarin jihadin suke.
Motoci ba sa iya shiga yankunan, don haka ba za ka iya tura jami’ai ba wajen saboda da motoci suke amfani kawai babu wani abu bayan nan.
Babu kayan aiki irin su kyamarori da jirage marasa matuƙa da za su taimaka wajen tattara bayanai kan wadannan mayaƙa.
- Juyin mulkins soji a Nijar ya haifar da koma baya a haɗinkan da ƙasashen biyu ke da shi.
A baya akwai jami’an tsaron Nijar a kan iya kar ƙasashen biyu “amma yanzu sojin sun janye sun mayar da su Yamai, don su basu tsaro a cikin gida gudun kar a kai musu hari,” in ji Malam Kabiru Adamu.
Yadda za a magance matsalar tsaron kan iyaka
Ƙarfafa tsaron iyakar ƙasashen biyu na da matuƙar muhimmanci, kamar yadda masana ke faɗa a ko da yaushe.
A wajen Dr Bulama Bukarti, idan kasamar da tsaro a wannan iyaka, “tamkar ka magance kashi 70 ne na matsalar da ake fama da ita ta tsaro.
“Makamai ba za su shiga ƙasashen ba kamar yadda suke shiga yanzu ba. Kwayoyi ba za su shiga ba kamar yadda suke shiga a yanzu ba. Kuma za a daƙile zirga-zirgar ‘yan bingidar da ke shiga Nijar daga Najeriya da kuma wadanda suke shiga daga Nijar zuwa Najeriya.
Ƙarfafa tsaro tsakanin Najeriya da Nijar
A baya ƙasashen biyu na aiki kafaɗa da kafaɗa da juna wannan ya sa an samu tsaro mai ƙarfi a lokacin.
Irin wannan alaƙa a baya ta cece yankunan biyu a baya, musammam a yankin arewa maso gabas lokacin da aka ƙirƙiri rundunar Multinational Joint Task Force, ta ƙasashen Kamaru Najeriya Nijar da kuma Chadi.
Dr Bulama ya ce da za koyi darasi daga abin da ya faru a kan Boko Haram wataƙila da an cimma nasara mai yawa.
“Tun da aka fara wannan rikici na arewa maso yammaci ka ji Gwamnatin Najeriya ta nemi ta Nijar domin yin aiki tare? Ya kamata a ce an ƙafa irinta a arewa maso yamma,” in ji mai nazarin.
Alaƙar Soja da Musayar bayanai tsakanin Nijar da Najeriya
A baya akan musanya bayanai tsakanin ƙasashen biyu, hakan ya kai su ga nasara a wasu ayyukan da suka yi a baya.
Da juyin mulkin da aka yi sai ‘yar alaƙar da ake da ita ta ƙarasa gurguncewa, saboda abubuwan da suka riƙa faruwa kan saka wa Nijar ɗin takunkumi.
A ɓangaren aikin soji tare da za a riƙa yi tare da samar da bayanai da babu wani wanda za a nema ya tserewa komar gwamnatocin ƙasashen biyu, in ji malam Kabiru.
To amma ba a da wannan alaƙar don haka kowa abin da yake gabansa yake yi, kuma masu iya magana na cewa biyu ta fi ɗaya.
“Idan so samu ne su kafa ofisoshi tsakaninsu a kan irin wadannan iyakokin”.
Dole a ƙarfafa sintiri a tsakanin yankunan domin da shi ne za a dakile fice da shigen mayaƙan.
Kuma idan suka ga ana kaiwa da kawowa to hakan zai sa su zama sun shiga taitayinsu in ji masana harkokin tsaron.
A samar da sansanonin duba mutanen da ke shige da fice wanda zai rage shiga da makamai ƙasashen biyu.
Da yawan yaƙin da ake yi da masu laifuka a duniya ya sauya salo, in ji Malam Kabiru.
“Aiki ake da kyamrorin ɗaukar bayanai da kuma jirage marasa matuƙa da za su iya tattara maka bayanai cikin ƙanƙanin lokaci kuma masu fa’ida da za su kai ka da nasara.
“Za su taimaka wajen gano su wanene suke shige da fice a kan iyakokin Najeriya da Nijar.”
Bulama Bukarti ya ce akwai bayanan sirri da ke cewa Lakurawa na da irin “jiragen nan marasa matuƙa kuma suna aiki da su sosai”.