A ranar Asabar Gwamnatin Vietnam tace, sun amince ita da China su karfafa hadin guiwa domin bunkasa sha’anin tsaro da kare kansu, duk kuwa da lokacin da suka dauka suna yar tsama da juna kan batun kogin kudancin China.

China ce dai abokiyar huldar kasuwanci mafi girma ga Vietnam, kuma babbar kafar da take shiga da kayayyakin sarrafawa a masa’antu cikin kasar ta.

Hakazalika kasashen biyu, sun amince a Ranar Asabar su bunkasa huldar tattalin arziki a tsakanin su, inda China ta sha alwashin kara bude kofar kasuwannin ta ga kayayyakin amfanin gonar kasar ta Vietnam, yayin da ita kuma Vietnam din zata bunkasa zuba hannun jarin ta a China, kamar yadda wata sanarwar gwamnati ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa, kasashen biyu zasu bada muhimmanci ga hadin guiwar bunkasa layukan jirgin kasa.

Sanarwar tazo ne bayan da Pirimiya Li Qiang na China ya gana da Shugaban Vietnam To Lam, a Hanoi da yammacin Asabar, a yayin da Li din ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a Vietnam.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kafar labaru ta Reuters cewa, ana sa ran a yayin ziyarar, China da Vietnam su rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da ya hada da wadda zata bunkasa aikin layukan dogo, da kasuwancin amfanin gona.

A ranar Lahadi ake sa ran Li zai gana da Priministan Vietnam Phan Minh Chinh, ya kuma halarci wani taron kasuwanci a Hanoi.

A farkon watan nan ne Vietnam tayiwa China bore kan abinda ta kira, hari kan jirgin kama kifin Vietnam a kan ruwan kudancin China da ake takaddama a kan shi, da ya yi sanadiyyar raunata masunta da dama.

By Ibrahim