Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta sake ɗaukar matakin ƙwace takardar izinin ɗan ƙasa ga ƙarin wasu mutum biyu mukusanta ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
An soke takardun ‘yan ƙasar mutanen biyu ne bayan an zarge su da aikata wasu ayyuka da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya, tsaro, addini da ƙyamar baƙi.
Mutanen uku da gwamnatin ta soke wa takardun zama ɗan ƙasa sun haɗa da: Mamman Sani Ali Adam wanda ɗalibi ne Busada Ben Ali wani ɗan jarida.
Wannan dai shi ne karo na uku da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ke ɗaukar irin wannan mataki na ƙwace takardun izinin zama ɗan ƙasa ga wasu ‘yan ƙasar.
Haka nan gwamnatin mulkin sojin ta soke takardun zama ƴan ƙasa ga kusan mutum 20 tun bayan kifar da gwamnatinsa cikin watan Yulin 2023.
Wannan mataki a lokuta da dama ya haifar da muhawara tsakanin ‘yan ƙasar kan dacewarsa ko akasin haka.
Me matakin ke nufi?
Farfesa Djibril Abarchi, tsohon malami a fannin koyar da darussan dokokin shari’a na jami’ar Abdoul-Moumouni Dioffo da ke birnin Yamai, ya ce abin da matakin ke nufi shi ne a ƙwace wa mutum matsayinsa na kasancewa ɗan ƙasa.
”Abin da hakan ke nufi shi ne ka koma matsayin baƙo a ƙasarka, saboda duk wani haƙƙi da ɗan ƙasa ke da shi, to kai ba ka da shi”, in ji tsohon malamin.
Ya ƙara da cewa ba wai ana nufin mutum ba zai zauna a ƙasar ba ne, zai zauna ne amma a matsayin baƙo.
”Cikin zaman nan na baƙunta da yake yi, idan ya aikata wani laifi, gwamnati na iya kai shi kotu, kuma kotun ka iya ce masa ba ta son sake ganinsa a wurin da yake ko ma ƙasar baki-ɗaya”, in ji shi.
Kenan dai hakan na nufin ƙasa za ta iya korar mutum daga cikinta, idan ta ƙwace masa takardun izini.
Wane laifi mutum zai yi a ƙwace masa takardar izini?
Farfesa Djibril Abarchi, ya ce kowace ƙasa tana da dokokin da ta tsara na ƙwace takardun izinin zama ɗan ƙasa ga mutane, idan suka aikata wasu laifuka.
Ya ce tun 1984 Nijar ke da tsarin irin wannan doka, kafin gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta yi wa dokar gyaran fuska a shekarar da ta gabata.
Tsohon malamin jami’ar ya ce daga cikin tsoffin dokokin, akwai tanadin cewa duk ɗan ƙasar da ya shiga aikin soji a wata ƙasa, aka ce masa ya janye ya ƙi, to ya aikata laifin da za a iya ƙwace masa takardun izini.
Haka ma idan mutum ya shiga cikin gwamnatin wata ƙasa, ma’ana ya karɓi matsayi, nan ma aka buƙaci ya janye ya ƙi amincewa, doka ta bayar da damar ƙwace masa takardun izini.
A ranar 27 ga watan Agustan 2024, gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta yi wa dokar gyaran fuska inda ta tanadi buɗe shafi ko fayil ga mutane ko ƙungiyoyin da ake zargi da ayyukan ta’addanci ko wani laifi da ya shafi tayar da hankalin jama’a.
Ta ya mutum zai dawo ɗan ƙasa bayan ƙwace masa takardu?
Farfesa Abarchi ya ce a tsohuwar dokar ta yi tanadin cewa za a mayar wa mutum takardunsu idan aka gindaya masa wasu sharuɗa sannan ya cika su.
”Amma a wannan sabuwar dokar, sharuɗanta daban suke, saboda idan aka kai mutum kotu, sannan ta wanke ka daga zarge-zargen laifukan da ake yi maka, to za a iya mayar maka da takardunka”, in ji tsohon malamin jami’ar.
Ra’ayin masana
Abdou Lokoko shugaban ƙawancen ƙungiyoyin farar hula na Rosen ya ce babu wata matsala tunda doka ce ta tanadi hakan, ”Duk abin da doka ta tanadar kuma aka yi shi bisa doka, to sai mu ce alhamdullahi”.
Ya ce hakan zai taimaka wajen rufe bakin mutanen da ake ganin suna haifar da ruɗani a ƙasar.
”Ai dama shi tsaron ƙasa ba a yinsa da wasa”, in ji shi.
To sai Abdulnasir Nahantsiyori mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum ya ce hakan bai dace ba.
Ya ce abin da gwamnatin mulkin sojin ke yi ya saɓa wa dokokin duniya.
”Duka manya-manyan dokokin duniya da Nijar ta yi na’am da su, idan aka yi la’akari da su, za a fahimci cewa abin da jagororin mulkin sojin ke yi ya saɓa wa dokokin”, in ji shi.
Ya ce kamar yadda sojojin ke iƙirarin cewa doka ce ta ba su dama, su ma dokar ce ta ba su damar sukar gwamnati.
”Don mutum ya bayyana ra’ayinsa da bai yi wa masu mulki daɗi ba, to bai kamata masu mulki su riƙa ɗaukar irin waɗannan matakai a kansu ba”.