Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin harshen al’umma a hukumance. Wannan na ɗauke ne a cikin wani kundi da aka saki a ranar 31 ga watan Maris na 2025, wanda ke ƙunshe a cikin tsarin gwamnatin ƙasar na 2025.
Bisa kundin: “Hausa ce harshen al’ummar,” kuma “harsunan aiki su ne Ingilishi da Faransanci.”
Kundin ya kawo jerin wasu ƙarin harsuna a cikin gida wanda suka haɗa da Zarma-Songhay, Fula, Kanuri, Gourmanche, da Larabci a matsayin “harsunan da ake magana da su a Nijar.”
Wannan ya biyo bayan wani taron ƙasa da aka gudanar a watan Fabrairu, wanda ya samar da shawarwari ciki har da wanda ya bai wa Abdourahamane Tchiani damar ci gaba da mulkin ƙasar har zuwa shekarar 2030.
Ma’anar Hausa a matsayin harshen al’umma
Tun kafin sanarwar, harshen Hausa ya zamo wanda kusan kowa na yinsa a ƙasar, musamman a yankunan Zinder, Maradi da Tahou. “Fiye da kaso 90 na al’ummar ƙasar miliyan 26 suna magana da harshen Hausa. Saboda haka ba za ka kwatanta shi da harshen Faransanci ba wanda mutum miliyan uku ne kawai suke iya amfani da shi,” in ji Tahir Guimba, jami’in gwamnati a Nijar.
Ya ƙara da cewa “bambanci yanzu shi ne Hausa ta zama harshen al’umma a hukumance, saɓanin a baya. Yanzu, Hausa ce harshen kasuwanci da cinakayya da kuma addini.”
Ƴan jamhuriyar Nijar za su iya gudanar da harkokinsu a cikin harshen Hausa bisa doka, duk da cewa harshen aiki na hukuma shine Ingilishi da Faransanci,” in ji Guimba.
Farfesa Abdou Majingini, masanin harsuna a birnin Yamai, ya ce “ayyanawar ta ƙara tabbatar da matsayin Hausa a matsayin harshen al’umma a Nijar.” Ya yi nuni da cewa “yanzu an tabbatar da yunƙurin gudanar da harshen haɗin kai a ƙasar.”
Farfesan wanda ya rubuta ƙamus na Faransanci zuwa Hausa ya ce “harshen Hausa ya kamata ma ya zama ɗaya daga cikin harsuna biyu da aka ayyana a matsayin harsunan aiki.”
Me ya janyo ayyanawar a yanzu?
Gwamnatin sojin ta jamhuriyar Nijar ta ce ta ɗauki matakin ayyana Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki da Hausa a matsayin harshen al’umma, a ƙoƙarinta na raba kanta da tsohuwar uwar gijiyarta – Faransa, tun bayan juyin mulki na 2023.
Nijar ta kuma ɗauki matakai irin su korar rundunar tsaron Faransa daga Nijar, da sauya sunayen tituna da wuraren tarihi da ke ɗauke da sunayen Turawan Faransa.
A yanzu, jamhuriyar Nijar tare da sabbin ƙawayenta – Mali da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar ƙasashe renon Faransa.