Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pavel Durov ya ƙirƙiro Telegram a 2013

Ana sa ran ɗan ƙasar Rashan nan, mai shafin sada zumunta da muhawara na Telegram, Pavel Durov, zai gurfana a gaban kotu a yau Lahadi.

Kafafen yaɗa labaran Faransa sun ruwaito cewa a jiya Asabar ne aka tsare hamshaƙin attajirin bayan da jirginsa ya sauƙa a filin jirgin sama na Le Bourget, da ke arewacin Paris.

Ana ganin an kama Mista Durov ne, mai shekara 39, saboda ya ƙi bayar da haɗin kai ga masu bincike kan yadda wasu masu aikata miyagun laifuka, ke amfani da manhajar ta Telegram.

Jami’an Rasha da ke ƙoƙarin samun bayanai kan dalilin kama shi, sun ce Faransa ta ƙi ba su haɗin kai.

Mista Durov, wanda aka haife shi a Rasha, kuma yake da takardar ɗan ƙasa ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Faransa, yana zaune a Dubai.

Mutum kusan miliyan 900 ne ke amfani da manhajar ta Telegram a faɗin duniya.

Kuma tana da farin jini sosai a Rasha da Ukraine da sauran ƙasashe na tsuhuwar Tarayyar Soviet.

An haramta amfani da manhajar a Rasha a 2018, saboda Mista Durov ya ƙi bayar da bayanan masu amfani da manhajar, amma kuma a 2021 aka ɗage wannan haramcin.

Telegram na ɗaya daga cikin shafukan sada zumunta da muhawara da suka fi fice a duniya, bayan Facebook da YouTube da WhatsApp da Instagram da TikTok da Wechat.

By Ibrahim