Asalin hoton, Getty Images

Bayanai na cewa ana can cikin damuwa, dangane da batun wasu manoma 21 da ‘yan bindiga suka sace a garin Bena na yankin ƙaramar hukumar Danko-Wasagu na jihar Kebbi.

An sace manoman ne yayin da suke aiki a gonakinsu a farkon wannan mako.

Jama’ar yankin na Danko Wasagu ta gabas dai sun kwashe tsawon aƙalla shekara biyar suna fama da wannan matsala ta hare-haren ‘yan bindiga.

Tun da ‘yan bindigar suka sace manoman daga gonakinsu, a garin Bena na yankin karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, ake dakon jin duriyar inda aka yi da su. Amma har yanzu ba amo ba labari, a cewar wani mutumin yakin.

Ya shaida wa BBC cewa kwana kusan biyar da ɗauke mutanen amma har yanzu shiru.

Matsalar hare-haren da ‘yan bindigan ke kai wa yankin na Bena dai ta kai intaha kamar yadda wani mazaunin garin ya ce.

A cewarsa akwai ƙauyuka da dama da ɓarayin daji suka mamaye kuma sun hana mutane zama ko ma zuwa gona.

Dangane da matakan tsaro da ake ɗauka, game da wannan matsala ta ‘yan bindiga, sai mutumin na yankin Bena ya ce ana ɗaukan matakai amma ba su wadata ba.

Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta kawo masu ɗauki domin cire su daga ƙangin da suka tsinci kansu ciki.

Mun dai yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar ta Kebbi, game da manoman ashirin da daya da ‘yan bindiga suka sace a yankin na Bena. Amma bai amsa kiraye-kirayen da muka yi masa, da saƙon da muka aika masa a rubuce ta waya ba.

By Ibrahim